Rundunar ‘yansanda ta haramta aibata jami’anta a fina-finai

Babban Sifeton ‘yan sandan Nijeriya Usman Alkali
Babban Sifeton ‘yan sandan Nijeriya, Usman Alkali Baba, ya gargadi masu shirya fina-finai a kasar da su guji aibanta aikin ‘yan sanda a shiryeshiyensu na telebijin, ba tare da izinin rundunar ba.
Usman Baba ya kara da cewa, daga yanzu kada a kara ganin wani mutum sanye da kayan ‘yan sanda a fina-finai, ba tare da izini ba kamar yadda doka ta tanadar. Ya ce, idan ba haka ba, to kuwa duk wanda ya karya doka zai dandana kudarsa.
Masu shirya fina-finai a Nijeriya kan kwaikwayi jami’an ‘yan-sandan kasar, kuma a mafi yawan lokuta ba a nuna su a mutanen kirki.
Sanarwar da rundunar ‘yan-sandan ta fitar ta ce, “kada wani mai shirya finafinai da ya sake nuna ‘yan sanda a matsayin marasa kirki ba tare da izini ba a rubuce daga rundunar ‘yansanda.”
Sanarwar ta kara da cewa, ba za ta amince da bayyana aikin ‘yan-sanda ba a fina-finai, matsawar abin da aka kwaikwaya a aikin ba shi da kyakkyawan tasiri ga al’umma