Rungumar noman zamani:Madaba’ar Triumph ta jinjina wa mata manoma

Daga Mahmud Gambo Sani
Shugaban mada’abar jaridun Triumph, Malam Lawal Sabo Ibrahim ya yaba da yunkurin kungiyar kananan manoma mata ta Nijeriya reshen jihar Kano wajen inganta da zamanantar da aikin gona da samar da aikin-yi a tsakanin manoma mata a jihar Kano.
Malam Lawal Sabo ya yi yabon a lokacin da shugabannin kungiyar karkashin jagorancin Hajiya Dije Ibrahim Sa’id suka kai masa ziyarar girmamawa a ofishinsa.
Shugaban ya yaba wa yunkurin matan na rungumar sana’ar noma, inda ya bayyana yunkurin da cewa, abu ne mai kyau lura da yadda gwamnatin tarayya da na jihohi suke kokarin bunkasa harkar noma wajen mayar da shi sana’ar da za a sami kudi masu yawa daga gare shi.
Ya kara da cewa, “ irin wannan noma na samun kudi ba zai yiwu ba sai da kayan aiki na zamani, dole ana bukatar injina na zamani wadanda za su maye gurbin kayan aiki na gargajiya. Wannan yunkurin naku na tashi daga kayan noma na gargajiya zuwa na zamani abu ne mai kyau, lura da yadda mata suke da kokari wajen alkinta abin da aka ba su domin inganta sana’arsu”
Daga bisani ya yi alkawarin tallafa wa kungiyar wajen ganin ta cim ma nasarorin da take bukata a bangaren bunkasa aikin noma.
Tun da farko da take jawabi, shugabar kungiyar, Hajiya Dije Ibrahim Sa’id ta ce, a wannan lokaci mata sun yunkuro wajen bunkasa harkar noma, inda suke amfani da kudadensu domin yin sana’ar.
Ta kuma bayyana cewa, a yanzu ‘yan kungiyarsu sun rungumi noman zamani da kuma amfani da kayan aiki na zamani, inda suka yi watsi da noman fartanya da garma domin inganta nomansu da kuma samun riba mai yawa.
Sai dai ta koka bisa yadda maza suka kankane duk wadansu harkokin tallafi da gwamnatoci suke bayarwa, inda ta yi rokon gwamnatoci da su rinka kula da mata a duk lokacin da irin wannan tallafi na noma ya taso domin saka mata a ciki.