Rushe Kasuwar Mata a Zariya: ‘Yan-kasuwa sun maka Karamar hukuma a kotu

Nasir-El-Rufai

Tura wannan Sakon

Labarai Isa A. Adamu Daga Zariya

Saboda yunKurin da mahukutan Karamar hukumar Sabon gari a jihar Kaduna suka yi na ba ‘yan kasuwar wa’adin kwana bakwai su kwashe ya – nasu – ya nasu domin yanke hukumcin rushe kasuwar, Kungiyar ‘yan kasuwar sun kai Karar makumtan Karamar hukumar Kara babbar kotun jihar Kaduna, domin kotun ta yi a su ganDo a tsakaninsu da Karamar hukumar ta Sabon gari.

A ranar larabar da ta gabata, babban mai shari’a a kotu na biyu da ke Unguwar Turawa [ GRA ], Mai Shari’a Rabi Salisu Oladoja , ta fara sauraron Karar ‘yan kasuwar Mata a wannan kotu, domin duba kukan da ‘yan kasuwar suka yi a bias jagorancin lauyansu Barista Dokta Bello Ibrahim Jahun, sun buKaci kotun da ta saurari kukansu kan matsalar da mahukumtan Karamar hukumar Sbon gari suka tsoma su.

Bayan sauraron lauya Barista Bello Jahun, sai mai shari’a Rabi Ladoja ta nemi lauyar da ke wakiltar Karaar hukumar Sabon gari ta yi tsokaci na batun da lauyar ‘yan kasuwar kasuwar mata suka gabatar a wannan kotu.

Ba tare da Bata lokaci ba, sai lauya da ta ke Karamar hukumar Sabon gari Barista Jummai Al’asan ta bayyana wa mai shari’a Ladoja cewar, lallai an kai wa Karamar hukuma takardar Karar da ‘yan kasuwan suka kai mahukumtan Karamar hukumar, ama, a cewar ta, ba ta kamala gabatar da jawabin kariya ba, sai ta nemi kotun ta Dage ci gaba da sauraron shar’ar, domin ta sami damar gabatar da bayanin kariya ga wannan babbar kotu.

Jin haka, sai mai Shari’a Rabi Salisu Ladoja, ta amince da buKatar lauyar da ke kare Karamar hukumar Sabon gari ta Dage ci gaba da sauraron Karar ya zuwa ranar shida ga watan Afirilun shekara ta 2022.

Bayan fitowa daga cikin kotun, wakilinmu ya nemi jin ta bakin lauyar da ke kare mahukumtan Karamar hukumar Sabon gari da suka haDa da shugaban Karamar hukumar da Sakataren Karamar hukumar da kuma jami’in da ke kula da sashin filaye na Karamar hukumar, sai lauyar ta shaida wa wakilinmu cewar, a matsayin ta na ma’aikaciya ma’aikatar shari’a ta jihar Kaduna, ba ta da damar da za ta yi Magana da manema labarai.

Shi ko lauya da ke wakiltar ‘yan kasuwan, Barista Bello Jahun ya ce, sun gabatar a wannan Kara ne, domin kotu ta dakatar da mahukumtan Karamar hukumar Sabon gari, da rushe wannan kasuwa ta Mata, har zuwa lokacin da kotu za ta kammala sauraron Bangarorin biyu, daga nan, a cewar Barista Jahun, sai ko wane Bangare ya san matsayinsa na hukumcin da kotun ta yanke.

Birista Bello Jahun ya Kara da cewar, a Karar da ya gabatar a madadin ‘yan kasuwan, ya buKaci kotu da ta umurci Karamar hukumar Sabon gari da ta biya ‘yan kasuwar Mata tsabar kuDi Naira Miliyan dubu Day da miliyan Dari biyar ko kuma ko wane rumfa da Karamar hukuma za ta rushe, ta biya ko wane Dan kasuwa da ya mallaki rumfa Naira miliyan bibbiyu ko wannensu, Wasu daga cikin shugabannin ‘yan kasuwan da kuma ma su rumfuna a kasuwar da suka haDa da Alhaji Shitu Maraya da Alhaji Yusuf Maja da Mada Maman Sharon da Alhaji Shitu Maraya dukkansu sun bayyana wakilinu cewar, mafiya yawansu sun shafe shekara 45 a cikin kasuwar, sun a biyan kuDin shiga ga Karamar hukumar Sabon gari , amma, sai suka wayi gari da bayanin su bar kasuwar a cikin kwana bakwai.

Sun Kara da cewar, doin neman mafita daga matsalar da suka shiga, sun kai kukansu zaBaBBun ‘yan siyasa da suka haDa da Dan majalisar tarayya mai wakiltar shiyya ta Daya, Alhaji Suleiman Abdullahi Kwari da na wakilai, Alhaji Garba Datti Babawo da na jihar Kaduna Alhaji Ali Usman Baba, dukkansu sun ce za su sa baki, a cewarsu, sai suka wayi gari da karBar takardar barin harabar kasuwar daga Karamar hukumar Sabon gari, wanda a cewrsu, bas u nuna damuwarsu da matsalar da suka kai ma su ba. Kafin rubuta wannan rahoton, wakilinmu ya yi KoKarin ganin ya ji ta bakin ‘yan majalisun da aka ambata, al’amarin ya ci tura

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *