Sabanin sauran fadar masarautu -Fadar Machina gabas take fuskanta

Sarkin Machina
Yusuf M. Tata Damaturu
Mafi yawancin fadar sarakuna a arewacin kasar nan suna fuskantar yamma ne, amma fadar sarkin Machina da ke jihar Yobe, Alhaji (Dokta) Bashir Albishir Bukar Machinama gabas take fuskanta.
A cikin wata ganawa da sarkin ya yi da manema labarai a fadarsa da ke Machina, ya bayyana cewa, an yi wani sarki a kasar Ngazargamo wanda yake da bukatar haihuwa, musamman da namiji, kasancewar ba shi da magaji idan ta Allah ta kasance gare shi.
Wannan sarki a cewar sarkin na Machina, ya tara malamai da sauran masana a kan wannan matsalar ta rashin haihuwa, inda suka dawo masa da amsar cewa, zai samu magaji, amma matar da za ta haifa masa magajin tana yamma da masarautarsa cikin duwatsu.
Ita wannan mata ta kasance matar wani maharbi ce, kuma su kadai ke zaune a wannan dutse. Wannan dutse dai ya kasance dutsen da ke kusa da gidan sarkin Machina ta gefen arewa.
Samun wannan labari da malamansa suka ba shi, sai ya umurci manyan fadar da nemo masa wannan matar, inda suka yi ta tafiya ba su tsaya a ko’ina ba sai da suka sami dutsen Dala da ke Kano, a tsammaninsu a nan matar take, amma ba su ga alamar mace a gurin ba, sai suka ya da zango suna hutawa, zaman hutawarsu ya sa wasu matafiya suka isko su, inda suka tambaye su, suka ce masu, ai kun baro wannan mata a baya, sai su ka kwatanta masu dutsen, inda suka runtumo zuwa ga wannan dutse da ke Machina a yanzu.
A nan suka sami wannan mata suka yi sa’a kuwa mijinta ba ya nan, suka dauke ta zuwa gidan sarkin Ngazargamu. Kamar yadda sarkin Machina ya zayyana wannan mata, an dauko ta da cikin watanni uku, saboda haka, bayan watanni shida sai ta haifi da namiji, inda aka rada masa suna Ali.
Shekara da ta zagayo sai wannan mata ta sake haihuwar da namiji, shi ma aka rada masa suna Ali, watau Ali karami da Ali Babba. Mutuwar sarki ke da wuya, aka nada Ali babba a matsayin sarkin Ngazargamo.
Nadin sarki Ali Babba bisa sarautar kasar Ngazargamo ta zo da matsaloli masu tarin yawa, inda bala’i ya dinga aukawa a kasar, har ta kai ga manya sun fara tunanin menene musabbabin wannan bala’in da ke addabar jama’a a kai a kai, har labari ya je kunnen mahaifiyar sarki Ali, sai ta sa aka kira mata masu ruwa-datsakin masarautar, ta fada musu cewa, wannan sarki (Ali Babba) ba danku ba ne, dan mijina na aure ne, saboda haka idan kuna son zaman lafiya sai kun cire shi daga sarauta, ku bayar da sarauta ga kaninsa.
Hakan kuwa aka yi, inda aka nada kaninsa Ali Karami bisa mulkin Ngazargamo, sai komai ya dawo daidai. Sarki Ali (Babba) ya dauki mutanensa, ciki har da limamin garin da sauran masu sarautar fadar, ya nufi yamma, har ya kai ga inda aka dauko mahaifiyarsa watau dutsen Machina, a nan ya bayar da umarnin a gina masa fada a wurin da fadin cewa, kofar ta fuskanci gabas, saboda ya dinga kallon masarautar kaninsa da ke gabas.
“Wannan shi ne ya sa har yanzu muka bar wannan fada da kofarta na kallon gabas”, inji sarkin Machina Alhaji (Dokta) Bashir Albishir Bukar Machinama. Sarkin ya ci gaba da cewa, “yanzu haka duk wuraren da nake zama in dai ya shafi na zaman sarauta ne, to na mayar da shi yana fuskantar gabas, saboda mu dora a kan abin da kakanninmu suka yi, kuma haka abin zai kasance ko da bayanmu.