Saboda digirgire: Ronaldo ya roki Man-United da ta sallame shi

Saboda digirgire: Ronaldo ya roki Man-United da ta sallame shi

Ronaldo ya roki Man-United da ta sallame shi

Tura wannan Sakon

Cristiano Ronaldo ya bukaci kungiyar da yake dokawa wasa yanzu haka Manchester United da ya yi wa Allah ta barshi ya yi gaba, muddun har ta samu tayin da ya dace da shi.

Dan wasan gaban na Portugal, mai shekaru 37, ya koma Old Trafford daga Jubentus a bazarar da ta wuce.

Duk da cewa Ronaldo, shi ne dan wasan da ya fi zura kwallo a raga a kakar wasan da ta wuce – kuma na uku a gasar Premier – ana kallon kakar wasannin da ta shude a matsayin babbar koma baya a gareshi.

United ta kare a matsayi na shida a teburin Premier don haka ta rasa tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai. Hakan na nufin Ronaldo, wanda ke da sauran kwantiragin shekara daya da United, zai fuskanci doka wasannin gasar Europa a karon farko.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *