Saboda gazawar ‘yar-jaridar fadar gwamnati: Buhari ya karbe ragamar yada labarai

Tura wannan Sakon

A ranar Talatar da ta gabata,Shugaban kasa Muhammadu Buhari,ya caccaki ‘yan-jarida saboda gazawa wajen yayata ayyukan raya kasa da gwamnatinsa ta aiwatar a sassan kasar cikin shekaru 7 kacal.

Ya furta haka ne a jihar Imo,a lokacin ziyarar kaddamar da ayyukan raya kasa da gwamnati ta aiwatar a jihar. Ya ce, ‘yan kalilan da ya iske a lalitar gwamnatin Nijeriya,ya yi amfani da su wajen raya kasa da farfado da tattalin arziki,kamar noma da masana’antu.

A cewarsa,daga shekara ta 1999 zuwa 2015, Nijeriya ta yi hauzi da miliyoyin dala, a sakamakon tashin kudin man fetur zuwa dala 100 a kan kowace gangar mai, domin haka,idan aka tuntubi babban bankin Nijeriya( CBN) da kamfanin mai na kasa ( NNPC),za a sami adadin kudaden suka tara a lokacin da ya ambata.

Duk da kudaden da gwamnati ta samu,babu abin kirkin da aka yi da su ta fuskar raya kasa da bunkasa tattalin arzikin kasa.

A karshe, shugaban ya ce, tilas ya karbe ragamar yada labarai daga ‘yan-jaridar gwamnati,dalili,tun da sun gaza” zan ci gaba da zama magori kan ayyukan raya kasa da gwamnatina ta sami nasarar aiwatarwa a sassan Nijeriya daban-daban.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *