Saboda hauhawar farashin kayan masarufi -Gidajen abinci sun yi karin farashi -In ji Abubakar

Gidajen abinci sun yi karin farashi
Daga Musa Diso
Manajan gidan abincin Shab`an da ke kan titin gidan Zoo, Malam Yahaya Abubakar ya bayyana hauhawar kayan masarufi musamman kayan abinci da cewa, wani babban kalubale ga ‘yan Nijeriya da ke fuskanta a wannan lokaci na rashin tabbas.
Manajan ya yi furucin ne ga wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano makon da ya gabata. Ya ce, sanin kowa ne cewa, al’ummar Nijeriya na bukatar tallafin gwamnati ta kowace fuska musamman wajen saukakawa jama`a domin gudanar da harkokin su na yau da kullum.
Ya kara da cewa, tabbas ya kamata shugabani da masu hannu da shuni su ji tsoron Allah kuma su tausayawa talaka kuma su dauki mataki domin agazawa ‘yan Nijiriya wajen bunkasa rayuwar al’umma da makamantansu.
Daga karshe, ya yi addu`ar Allah ya baiwa kasar nan zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma ci gaban al’umma kuma yana taya al’ummar musulmi kammala watan azumin Ramadan lafiya.