Saboda inganta tsari: Shugaban madaba’ar Triumph ya ciri tuta -Shugaban Mahauta

Shugaban Madaba’ar Triumph

Shugaban Madaba’ar Triumph

Tura wannan Sakon

Daga Salisu Baso

An bayyana ci gaban madaba’ar jaridun Triumph wajen buga ingantattun jaridu da samar da sahihan labarai, bisa kyakkyawan jagorancin shuganbanta, Malam Lawal Sabo Ibrahim.

Shugaban kungiyar mahauta na kasuwar Abubakar Rimi (Sabon Gari), Alhaji Musa Lawan Kakara ne ya bayyana hakan, a ganawarsa da Albishir, inda ya bayyana farin cikinsa da ci gaban da ake samu a kamfanin a kan lokaci.

Ya kara da jaddada goyon bayansa ga shugaban bisa samun nasarar, inda ya ce, kyakkyawan shuganbancin ya kawo daukakar jaridun wadanda ake bugawa cikin harsunan Turanci da Hausa da kuma Ajami, wajen samar da ingantattun labarai.

Alhaji Musa Kakara ya kara da cewa, madaba’ar jaridun mai tarihi da ta yi fice a Arewacin Nijeriya, wadda take share hawayen ’yan Arewa tun bayan rashin jaridun New Nigeria da Gaskiya ta fi Kobo, saboda haka ya yaba wa shugaban.

Ya kuma ce, jaridar ta Triumph na fito da ayyukan alkhairai da gwamnonin Arewa ke aiwatarwa, musamman a jihar Kano, na ayyukan gwamna Abdullahi Umar Ganduje a manyan ayyuka, saboda haka, ya jinjina wa shugaban madaba’ar. Alhaji Musa Kakara ya jaddada mahimmancin karatun jarida wajen ilmantarwa tare fadakarwa na aikaceaikacen

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *