Saboda karya ka’ida: CBN ta soke sayar da kudaden waje

CBN ta soke sayar da kudaden waje

Emefiele

Tura wannan Sakon

 Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ce, daga yanzu ya daina sayar wa ‘yan canji masu lasisin kudaden ketare kamar yadda ya saba saboda zargin rashawa da kuma damfara da yake yi wa ‘yan canjin.

Gwamnan Babban Banki Gowin Emefiele, ya zargi ‘yan can­jin da cewa, a maimakon gudanar da harkokinsu na kasuwanci, a yanzu sun rikide zuwa masu taimakawa domin yada rashawa a cikin harkokinsu.

Emefiele ya ci gaba da cewa, ‘yan canjin na taimaka wa masu gudanar da mum­munar harkalla da kuma halasta kudaden haram a Nijeriya, tare da alkawarin daukar mataki a kan masu aikata hakan.

Shugaban bankin wanda ke gabatar da jawabi a ka­rshen taron kwamitin tsara siyasar kudade na kasa (MPC) a birnin Abuja, ya ce, daga yanzu ba za a sake sayar wa ‘yan canjin kud­aden ketare ba kamar yadda aka saba ballantana sayar masu da sabon lasisi domin gudanar da harkokinsu.

Godwin Emefiele ya ce, a maimakon ‘yan canjin, yanzu CBN za ta yi hulda ne kai-tsaye da bankunan kasar tare da tabbatar da cewa, an samar da kudaden ketare a wadace ga wadan­da ke shigar da kayayyaki daga ketare zuwa cikin ka­sar, da sayen magunguna, biyan kudaden makaranta, yin tafiye-tafiyen da ba su saba wa doka ba da sau­ransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *