Saboda karya ka’ida: Kotu ta ci tarar Karota a Kano

Tura wannan Sakon

Babbar kotun jiha da ke Bompai a Kano ta umarci hukumar KAROTA ta biya wadansu mutane uku N500,000 kowannensu bayan da hukumar ta kama su da zargin yin goyo a baburansu.

Alkalin kotun mai shari’a Nasiru Saminu ya ce, a yanzu yin goyo a babur ba laifi ba ne a dokar kasa, matukar ba haya suke yi da baburan ba.

Watanni 18 ke nan da wadansu mutane tara suka shigar da karar hukumar ta KAROTA gaban koton, bisa kama su da suka yi domin kawai sun dauko iyalansu a bayan baburansu.

Bayan da aka shafe tsahon lokaci ana tabka shari’ar, alkalin ya yanke hukunci cewa, hukumar KAROTA ta aikata laifi da ta kama mutanen kuma ta umarceta da ta biya su diyya. Kotun ta umarci a biya mutane ukun farko diyyar N500,000 kowanne kan kama su da aka yi ba bisa ka’ida ba, sai kuma wata N100,000 kan bata masu lokaci.

Bayan yanke hukuncin ne lauyan wanda ke kare masu korafin, Barrister Abdulkareem Kabir Maude ya ce, kotu ta tabbatar da cewa, kowa zai iya goyo a kan baburinsa.

Ya kara da cewa, kotu ta yi umarci da a mayar wa wadanka aka ci tara kudadensu da aka karba kuma a biya su diyya. “Kotu ta ce, a dawo masu da kudadensu da aka karba, mutane ukun farko a biya su dubu 500 kowannensu, a kuma biya su kudin kara N100,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *