Saboda samun lambar yabo ta CIISec: MD Galady ya taya Pantami murna

Farfesa Isah Pantami, kogi matattarar ilimi -Farfesa Rasheed

Farfesa Isah Pantami

Tura wannan Sakon

Danjuma Labiru Bolari, Daga Gombe

Babban darakta na Galady Backbone, Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya taya ministan sadarwar zamani da tattalin arzikin kasa, Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami murnar samun lambar yabo ta (CIISec) Charted Institute of Information Security.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya taya ministan murnar ne ta bakin mai taimaka masa na musamman a bangaren yada labarai, Tasiu Muhammad Pantami, inda ya ce, ministan ya zama gwarzo abin a yaba masa.

Farfesan ya ce, minista Ali Pantami, ya ciri tuta domin yana cikin kalilan ‘yan Nijeriya da suka samu lambar yabon domin duk fadin kasashen Afirka su 89 ne kadai suke da irin lambar yabon.

A cewar Tasiu Pantami, ya bayyana ministan ne da hazikin minista wanda ya kawo wa kasarsa ci gaba mai ma’a a bangaren sadarwar zamani tun shigar ofis a matsayin ministan Nijeriya wanda ya mayar da hankali sosai a kan abin da ya shafi harkar tsaron kasa ta bangaren kimiyya da hakan kuma ya haifar da da mai ido.

Farfesa Muhammad Bello Abubakar, ya yaba wa cibiyar CIISec na yadda suka zakulo Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami ministan sadarwa ganin yadda ya mayar da hankali wajen ci gaban kasa da kula da harkar sadarwar yanar gizo domin ci gaban duniya baki daya suka karrama shi da lambar yabon. Daga nan ya ce, CIISec su kadai ne cibiyar kula da harkar sadarwa ingantacciya da suka samu izinin masarautar kasar Birtaniya tun a shekara ta 2018 da aka dora wa alhakin kula da kwarewar harkar da ta shafi bangaren sadarwa kuma su ne suka karrama ministan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *