Saboda sukar Annabi: Masar ta dakatar da farfesa daga aiki

An dakatar da wani Farfesan ilimin zamantakewa a Masar, bayan zargin da ake yi masa na yin batanci ga Annabi Muhammad (SAW) yayin da yake gardama da dalibansa kan batun aure a Musulunci, da kuma bayyana ra’ayinsa a kafar sada zumunta kan zanen batanci da Mujallar Charlie Hebdo ta yi ga Annabin.
Daliban koyon ilimin zamantakewar sun bayyana bacin ransu kan irin kalaman da Farfesa Muhammad Mahdali ya yi yayin da yake bayyana ra’ayinsa.
Tun da farko dai, daliban sun zargi farfesan da yin kalamai marasa dadi kuma na cin mutuncin Musulunci yayin da yake koyarwa a aji.
A wani bidiyo da aka yada a kafofin sada zumunta, an ga Farfesa Mahdaly na caccakar ayoyin Al-kur’ani a yayin da yake wata tattaunawa kan batun aure da biyan sadaki da kuma saki a Musulunci.
Daga baya kuma sai ya yi sa-in-sa da ɗalibai a lokacin da yake koyar da su a ji a yayin da suka nemi su taka masa burki kan irin kalaman da yake yi, inda suka ja masa kunne kan cewa ya daina haɗa kalamansa da Al-Ƙur’ani.
A wani bidiyo na daban kuma, an ga farfesan na caccakar yanayin zamantakewar Musulmai inda ya ce abin da suke yi “ba shi da asali”. Har ma ya kawo misali da auren mata tara da Annabi Muhammad (SAW) ya yi kuma ya yi kakkausar suka ga Annabin kan hakan.
Wannan katoɓarar da farfesan ya yi kan batun caccakar ayoyin Al-Ƙur’ani da kuma nuna goyon baya ga kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya harzuƙa mutane da dama musamman a kafofin sada zumunta, inda suke ta caccakar farfesan. Wasu daga cikin masu amfani da shafin Twitter sun alaƙanta farfesan da mutum mai laLurar “taɓin hankali”