Saboda zargin gano cutar daji: Nijeriya ta haramta shigo da taliyar Indomie –NAFDAC

taliyar Indomie

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna, Nafdac, ta ce za a iya cin taliyar indomie wadda ake sarrafa wa a gida, saboda ba ta dauke da sinadarin haddasa cutar daji.

Shugabar hukumar Nafdac, Farfesa Mojisola Adeyeye, ce ta bayyana haka yayin tattaunawa da BBC, inda ta ce, taliyar ta indomie da ta sahale a ci, a kasar ake samar da ita.

Farfesa Adeyeye ta ce, a shekarun baya, gwamnatin tarayya ta haramta shigo da indomie domin karfafa gwiwar masu samar da ita a cikin gida.

An yi ta samun rahotanni mabambanta cewa, taliyar indomie mai dandanon kaza da Taiwan da Malaysia ke samarwa, tana dauke da sinadarin Ethylene Odide da ke haddasa cutar daji. Sai dai, Nafdac ta ce, indomie da ake samarwa a cikin gida ba ta da wata alaka da ta Taiwan ko ta Malaysia.

Nafdac ta ce, ta fara gudanar da bincike kan taliyar kamfanin Indomie da kuma cikin kasuwannin Nijeriya. Wannan na zuwa ne bayan da Taiwan da Malaysia suka ce, wata taliya mai dandanon kaza na dauke da sinadarin da zai iya janyo cutar daji.

Nafdac ta ce, babu irin nau’in taliyar ta indomie a cikin kasuwannin Nijeriya, inda ta ce, za su yi gwaji domin gano ko wadansu vata-gari sun shigo da ita cikin kasar. Farfesa Adeyeye ta ce, taliyar indomie na cikin abubuwan da hukumar kwastam ta haramta shigo da su.

Batun sinadari mai jawo cutar daji da aka ruwaito cewa, indomie na dauke da shi ya janyo fargaba kan ingancin abinci a duniya ciki har da Nijeriya ganin cewa, indomie na cikin abubuwan da ake ci ko da yaushe.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *