Saboda zargin hadin baki: Jami’an tsaro na kwace mana abinci – Al’ummar Shinkafi

Tura wannan Sakon

Shu’aibu Ibrahim daga Zamfara

Jama’ar yankin karamar hukumar shinkafi ta jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya, sun fara kokawa dangane da matsalar karancin abinci da su ke fuskanta.

Wani mutumin yankin na Shinkafi ya shaida wa BBC cewa, duk da yanayi da ake ciki na karancin abincin, ana samun wasu jami’an tsaro na shiga cikin kasuwanni su kwace abincin da mutane ke saaya.

Mutum wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce,” Jami’an tsaro kan tare mutane idan sun tashi daga kasuwa ko sun sayi kayan abinci, sai su budea su ga me ka siya, wani lokaci su bar mutum ya tafi da abin da ya siya, wani sa’in kuma sai a raba abin da ka siya gida biyu a ba ka rabi”.

Ya ce,” Dalilin da ya sa jami’an tsaron ke yin haka kuwa shi ne suna tunanin cewa ka siya ne domin ka kai wa ‘yan bindiga. Mutumin ya ce,” A daidai lokacin da ‘yan bindiga suke hana mutane zuwa su noma abincin da za su ci, a lokacin ne kuma ake zargin wai mutane za su sayi abinci sukai musu, wannan sam ba hujja ba ce”.

Ya ce wannan shi ne irin halin oh ni ‘ya su da ake ciki a yankin karamar hukumar ta Shinkafi. A don haka muke kira ga gwamnatin jihar da ta kawo musu dauki,

saboda idan har an ha namu dibar abin da muka noma, to yakamata a bar mu muje kasuwa mu sayi abincin da za mu kai wa iyalansu inji mutumin. Ya ce ta ya ya za’ayi tunanin cewa mutumin da zai sayi abincin kwano-kwano, zai kai wa ‘yan bindiga?, yace ai su ‘yanbindigar sun san in da suke samunabincin da za su ci.

Ya ce,” Man fetir da aka hana sayar wa ‘yan bindiga bai hanasu hawa babura ba, a don haka baikamata jami’an tsaro su rinka zargin mutane na siyan abinci su na kai musu ba”. Mutumin ya ce a kodayaushe talaka shi ne a cikin mawuyacin hali wanda bai san in da zai sa kansa ba, duk wata doka da za a yi don ‘yan bindaga, to a kan talakawa take karewa.

Ya ce, “Idan har duk dokokin da ake yi domin ‘yan bindiga suna shafarsu, da farmamin da suke kai wa ba su kai ba, haka man da suke amfani da shi a babura, a ina suke samu?”.

Ya ce, ba wai ya na gwasale kokarin gwamnati Saboda zargin hadin baki: Jami’an tsaro na kwace mana abinci — Al’ummar Shinkafi ba ne, gaskiyar abubuwan da ke faruwa ya ke fada, a don al’ummar yankin ke neman daukin gwamnati a game da wannan damuwa ta su.

Ko da wakilinmu ya tuntubi kwamishinan da ke kula da harkokin tsaro na jihar don jin ta bakin gwamnati, a kan wannan batu da al’ummar yankin Shinkafin ke fada, duk kokarin hakan ya ci tura domin ba a same shi ta waya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *