Sabon Irin Tela Maize: Sheikh Bin Usman ya bukaci a tallafa wa hukumar IAR

Sheikh Bin Usman

Tura wannan Sakon

Isa A. Adamu Daga Zariya

A shirin da hukumar bunkasa dabarun noma na’’ INSTI­TUTE FOR AGRICULTUR­AL RESEARCH ‘’na samar da sabu­war irin masara da ake kirar ta sunan ‘’TELA MAIZE ‘’ fitaccen malamin addinin musuluncin nan da ke Kano Shekh Muhammad Bini Usman ya ya yi kira ga gwamnatin tarayya musam­man ma’aikatar bunkasa noma ta kasa da ta duba yiwuwar ba hukumar ‘’ IAR ‘’ yalwataccen kudi, domin ta sami damar fuskantar ayyukan bin­cike da aka dora wa mahukumtan hu­kumar.

Sheikh Bini Usman ya nuna wan­nan bukata ce a lokacin taron yini guda da hukumar ta shirya mai tak­en ‘’Gani ya kori ji’’ da ya gudana a gonar gwajin irin masara ta TELA MAIZE da hukumar ke kokarin kam­mala bincike sabon irin a shekara ta 2022.

Fitaccen malamin addinin musu­luncin day a kasance a gonar gwajin irin masarar da aka ambata, ya gane wa idonsa kokarin binciken da wan­nan hukumar ke yi, na samar da ma­sarar da manoman Nijeriya ba su taba samun irin masara mai kama da wan­nan iri na TELA MAIZE musamman in an duba ci gaban da manoma za su samu a noman da suke yi.

A game da yalwataccen kudi da Shehin malami Bini Usman ya bayar da shawarar a kara samar wag a huku­mar ‘’ IAR ‘’, Ya ce ya na da muhim­manci bayan gwamnati ta samar da kudaden ta kuma sa hajar mujiya na ganin lallai kudaden an yi amfani da su ta hanyar da aka bayr da kudaden, yin haka, zai sa duk kudaden da aka fitar al’umma, musamman manoma sun ga amfanin kudaden da aka fitar.

Da kuma Shekh Bini Usman ya juya ga mahukumtan hukumar ‘’ IAR ‘’ ya yi kira garesu da su yi tsarin da wannan sabon irin da za su fitar a shekara ta 2022, ya kai ga manoma na kauyeyn – kayau, a cewarsa, domin a nan ne manoma na hakika suke.

A karshe, Shekh Muhammad Bini Usman ya yi kira ga kungiyoyin da aka kafa su domin tallafa wa mano­ma, da su hada hannu da hukumar ‘’ IAR ‘’ domin sabbin binciken da suke yi ya kai ga manoma da kuma su tab­batar ya kai ga manoma da kuma sab­bin iraruwan da cibiyar ke samarwa a nan gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *