Sabon Sardaunan Katsina, ta leko ta koma

Sabon Sardaunan Katsina, ta leko ta koma
An dakatar sarautar sardaunan Katsina, sanarwa da Alhaji Sule Mamman Dee, sarkin tsaftar Katsina ya sanya wa hannu ta ce, nan gaba za a tuntube shi domin yi masa karin bayani.
“Bisa ga takardar da aka ba shi ranar 16/4/2022 wadda aka bai wa sarautar Sardaunan Katsina, majalisar Maimartaba sarkin Katsina ta umarce ni da na rubuto na sanar da dakatar da Sarautar.
Tun da farko farko, sarkin Katsina ya tabbatar masa da sarautar ne a cikin wata takarda mai dauke da sa hannunsa a ranar Asabar 16 ga watan Afrilu.
“Na amince da ba ka sarautar Sardaunan Katsina kamar yadda ka nema,” kamar yadda Sarkin Katsina ya bayyana a cikin takardar. Sanarwar ta ce, nan gaba za a sanar da ranar bikin nadin nasa.
Saddik jika ne ta bangaren uba ga sarkin Fadan Katsina, Isma’ila Damale wanda shi kuma da ne ga Wazirin Katsina na farko, Haruna Kaita.
Haka kuma ta bangaren uwa jika ne ga Makaman Katsina, Marigayi Tukur Idris Nadabo hakimin Bakori.
A kwanakin baya ne aka bai wa Ibrahim Ida sarautar Wazirin Katsina wanda a baya shi ne Sardaunan Katsina.
Wannan na zuwa ne bayan ajiye sarautar waziri da Alhaji Sani Lugga ya yi saboda wadansu dalilai