Sabuwar shekarar 2022: Gwamnan Wike ya ziyarci Bauchi domin nuna murna

Gwamnan jihar Ribas, Nyelsom wike tare da takwaransa Bala
Jamilu Daga Bauchi
Gwamnan jihar Ribas, Nyelsom wike ya bayyana irin kyawawan halaye na gwamna Sanata Bala Abdulkadir Muhammed (Kaura Bauchi) inda alakarsu ta kara karfi saboda haka ya zabi garin Bauchi a matsayin garin da zai kaiwa ziyara a ranar farkon sabuwar shekara, inda ya kara bayyana irin dadddiyar alaka da ke a tsakanin jihohin guda biyu.
Ya ci gaba da yaba wa da kambama irin na mijin kokarin da gwamna Kaura yake yi wajen gudanar da manyan ayyuka na raya kasa a jihar Bauchi.
Ya ce, tabbas irin wadannan halaye na gwamnan Bauchi abin koyi ne ga shugabanni a cikin jawabansa ya kara da cew, a irin matsalar tabarbarewar mulki da muke fama da shi a kasar nan ya samo sila ne daga rashin shugaba jajirtacce, shi yasa ko aiki idan ya bayar baya zuwa ya duba saidai abinda aka fada masa shi yasa yake kara misali da gwamna Kaura a kan jajirtacce ne kuma yakan ware lokaci ya bibiyi ayyukan da ya bayar a gudanar.
Kuma ya ayyana shi a matsayin matashi mai jini a jika wanda irin su ya dace su mulki kasar nan domin samar da ci gaba mai dorewa A jawabinsa gwamna Bala Muhammad ya gode wa takwarannasa na jihar Ribas bisa kambamawa da ya yi masa a kan irin ayyuka da yake gudanarwa a jihar Bauchi.