Sace-sace:Kanawa sun koka kan satar allunan makabartu

Masu kula da wata makabarta da ke Gwale a jihar Kano a Arewacin Nijeriya na ci gaba da kokawa kan irin yadda suka ce ana samun karuwar sace allunan alamomi na kaburbura.
Masu kula da makabartar sun shaidawa Albishir cewa, tun kusan watanni uku baya ne suka lura ana yi wa shaidar da ake sakawa kaburbura dauki dai-dai.
Yayin da wadansu kuma allunnan suke ganin su a lankwashe idan gari ya waye lamarin da kenuni da cewa, an yi kokarin cirewa ne amma hakan ta gagara.
Wakilinmu wanda ya je makabartar kafa da kafa, ya ce ya ga kaburbura da dama da aka cire allunansu aka tafi da su, wadansu kuma a allunan alamarsu a lauye.
Danjuma Labaran na daga cikin masu hakar kabari a wannan makabarta ta Dandolo, ya kuma bayyanawa Albishir cewa, tun da farko sun fara samun koke ne daga wajen jama’a dangane da batan allunan da suka sanya a kaburburan ‘yan uwansu da aka binne a makabartar.
‘’Muna zargin ‘yan gwan-gwan ne ke zuwa su kwashe su, domin su ne suke yawo a nan wajen, sukan zo su wuce, kuma akwai gefen makabarta da suke irin wadannan ayyukan’’ in ji Malam Danjuma.
Sai dai wadansu masu sana’ar ta tsince-tsincen kayan karafan, watau ‘yan gwangwan a wannan yankin, sun musanta wannan zargi da ake yi masu.
Jihar Kano dai na da tarin makabartu da dama da babu hasken wutar lantarki, abin da wadansu ke ganin cewa, kan taimaka wajen bayar da mafaka ga masu zuwa su aikata miyagun laifuffuka a cikinsu.
A wadansu lokuta a baya, an sha samun wadanda ke shiga makabartu a jihar da tsakar dare domin tone gawarwaki, su ciri wadansu sassan jikinsu da wata mummunar manufa.
Jihar Kano na da mai bai wa gwamna shawara na musamman kan lamuran da suka shafi makabartu, amma duk da haka wadansu ‘yan jihar na kokawa kan yadda ake samun matsaloli irin wadannan.