Sadik Ango Abdullahi Ya Sha Bamban Da ’Yan-Siyasa -Haj Zainab

Tura wannan Sakon

Daga Isa A. Adamu, Zariya

Wata futacciyar ‘yar siyasa da ke gundumar Bomo a karamar hukumar Sabon gari da ke jihar Kaduna, mai suna Hajiya Zainab Mohammed Bello, ta bayyana dan takarar majalisar wakilai a karkashin jam’iyyar PDP a karamar hukumar Sabon gari Alhaji Sadik Ango Abdullahi da cewar, dan siyasa ne da ya ke tare a jama’a ako wane lokaci, ba lallai, sai lokacin da aka kada kugen – siyasa ba.

Hajiya Zainab Mohammed ta bayyana haka ne a lokacin da ta amsa tambayoyin manema labarai kan wadanda suka fito takara a kujeru daban – daban daga wasu jam’iyyu a karamar hukumar Sabon gari, a zaben badi, wato shekara ta 2023.

Yar siyar ta ci gaba da ewar, duk wanda ya san Alhaji Sadik Ango Abdullahi a karamar hukumar Sabon gari, ya san shi dan siyasa ne da ako wane lokaci babu shamaki a tsakaninsa da al’umma, musamman wadanda ba ma ‘yan siyasa da ska hada da matasa maza da mata da yak e tallafa ma su a bangarorin da suka shafi ilimi da kuma sana’o’in dogaro da kai.

Wadannan halayen rungumar al’umma da Alhaji Sadik Ango ya ke da su shekaru da dama da suka gabata, a cewar Hajiya Zainab Mohammed Bello, ya sat un da al’umma suka nemi ya tsunduma harkar siyasa, ya zama kadangaren bakin tulu ga ‘yan siyasa da dama da suke karamar hukumar Sabon gari, na yadda halinsa na kula da al’umma fiye da yadda sauran ‘yan siyasa ke yi a shekaru da dama da suka gabata.

A kan haka ne, Hajya Zainab ta ce matukar al’ummar karamar hukumar Sabon gari na son ganin matsalolin da suka dabai – baye su sun zama tarihi, wajibi ne a garesu su zabi Alhaji Sadik Ango Abdullahi a kujerar majalisar wakilai a zaben shekara ta 2023, wanda zai zama matakin farko, a cewar Hajiya Zainab Bello, matsalolin da suka yi ma su kawanya, za su zama tarihi, domin sun zabi wanda ya san matsalolinsu shekaru da dama da suka gabata.

Da kuma Hajiya Zainab Muhammed ta juya ga takwarorin ta mata musamman wadanda ke karamar hukumar Sabon gari, ta shawarce da su yi taka tsan – tsan da wasu ‘yan siyasa da suka yi amannar kudaden da suka tara domin zaben shekara ta 2023, su ne za su yi sanadin nasarar da suke sa ran yi, bayan wannan zabe, kamar yadda ta ce, yin karatun baya na shekarun da suka gabata na ukubar da aka cusa su, ta ce zai matukar tasirin gane dan siyasa nagari, irin Alhaji Sadik Ango Abdullahi da ya saba tallafa wa al’umma, ba domin siyasa ba.

A karshen zantaar da Hajiya Zainab Mohammed Bello ta yi da manema labarai, ta kuma shawarci takwarorin ta mata, da su ci gaba da hada kansu domin, kamar yadda ta ce sai da hadin kan ne za su sami damar zaben ‘yan siyasa nagari, da za su dumfari matsalolin da suke addabar Nijeriya, musamman matsalolin tsaro da tsadar rayuwa da kuma matsaloli ma su yawan gaske.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *