Sadio Mane ya je Jamus domin kammala komawa Bayern

Sadio Mane

Tura wannan Sakon

Sadio Mane ya je birnin Munich ranar Talata, don kammala komawa Bayern Munich da taka leda daga Liberpol.

Sky ta saka wani faifan bidiyon dan kwallon a wani jirgi na kawa da ya isa birnin a shirin auna koshin lafiyar dan wasan tawagar Senegal.

Bayan auna koshin lafiyar dan wasan zai saka hannu kan yarjejeniyar kaka uku, inda mujallar Kicker sports ta ce za a gabatar da dan kwallon a ranar Laraba.

Mane zai koma buga Bundesliga kan yuro miliyan 32, ana cewa kudin zai kai yuro miliyan 41 idan aka hada da tsarabe-tsarabe.

Dan kwallon tawagar Senegal zai karfafa wasannin Bayern Munich, bayan da ake cewar ba a san makomar Serge Gnabry, sannan Robert Lewandowski na san zuwa Barcelona a kakar da za a fara a badi. Sau biyu Liberpool tana yin watsi da tayin da Bayern ta yi mata kafin ta amince ta sayar da dan wasan mai shekara 30, wanda kwantaraginsa da Reds za ta kare a bazara.

Liberpool ta saye shi daga Southampton a shekarar 2016 a kan £31m da karin £2.5m na tsarabetsarabe. Tun daga wancan lokacin, Mane ya zura kwallaye 90 a Gasar Firimiya a wasannin da ya yi wa kungiyar sannan ya kammala kakar wasan da ta wuce da cin kwallaye 23 a gasa daban-daban da ya yi wa Liberpool.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *