Sakataren gwamnatin tarayya ya kama aiki

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

A ranar Larabar da ta gabata, shugaban kasa, Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya rantsa da Sanata George Akume a matsayin sakataren gwamnatin tarayya. An yi bikin rantsarwar a gaban jami’an gwamnati a fadar gwamnati da ke Abuja.

Daga cikin wadanda suka halarci rantsar da sakataren gwamnatin sun hada da mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima, da shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan da gwamnan jihar Kwara AbdulRahman AbdulRazak da shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya, Dokta FolasadeYemi-Esan.

A makon da ya gabata, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayar da sanarwa da kansa kan nada Mista George Akume da Femi Gbajabiamila a matsayin sakataren gwamnatin tarayya da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati bi da bi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *