Sakon Sallah: Sarkin Potiskum ya jinjina wa Buhari, MaiMala -Saboda zaman lafiya

Mai Martaba Sarkin Pataskum, Alhaji Umaru Bubaram

Tura wannan Sakon

Daga, Sani Gazas Chinade, Damaturu

Mai Martaba Sarkin Pataskum a jihar Yobe, Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wurwa Bauya ya yaba wa shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni bisa kokarisu na kawo zaman lafiya a jihar Yobe da kasa baki daya.

Sarkin na Pataskum ya yi wannan yabon ne a cikin sakonsa na Sallah ga al’ummar masarautarsa ta Potiskum sannan ya bukaci jama’a da su yi wa kasa addu’ar zaman lafiya. Basaraken ya kuma bukaci al’umma da su kasance masu bin doka da oda tun daga kan kananan hukumomi da jiha da kuma gwamnatin tarayya wanda hakan zai ci gaba da samar da zaman lafiya da ci gaban kasa mai dorewa.

Sarkin ya kuma yaba wa manoma da makiyaya bisa kyakkyawar alakar da ke tsakaninsu, inda ya bukace su da su ci gaba da rike irin wannan alaka domin zaman lafiya da ci gaban kasa. Dagan an sai ya gode wa hakimai da dagatai da jaurawa bisa hadin kan da ke tsakaninsu, ya kuma ji dadi yadda manoman da makiyayan ke zaune lafiya da juna.

Ya kuma bukaci jama’a da su ci gaba da zaman lafiya da bin doka da oda domin zaben shekarar 2023 yana karatowa, inda ya bayyana cewa, zaman lafiya da ci gaban al’umma wani makami ne da ya dace domin samun nasarar zabe a kasar nan. Alhaji Umaru Bubaram Ibn Wurwa Bauya ya yi kira ga iyaye da jagorori da su rika tura yaransu zuwa makarantun Islamiyya da na Boko, inda ya ce, duk al’ummar da ba ta da ilimi to babu ci gaba a wurinta.

Ya bukaci jama’a da su ci gaba da yin addu’ar Allah ya karo albarkar noma a bana da kuma wadata jihar Yobe da Nijeriya baki daya.

Sarkin ya kuma yaba wa sojojin Nijeriya da sauran jami’an tsaro na kasar bisa kishin kasa da jajircewarsu wajen yaki da ta’addanci da sauran laifuka tare da samar da zaman lafiya a kasa baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *