Samar da fetur: IPMAN ta yi barazanar kawo cikas, muddin…

Samar da fetur: IPMAN ta yi barazanar kawo cikas, muddin...
Tura wannan Sakon

Kungiyar dillalan man fetur ta kasa IPMAN ta bayyana dalilan da suka haddasa cunkuson ababen hawa a gidajen mai, musamman a Abuja babban birnin tarayya da kuma wadansu jihohi, saboda abin da ta kira na dakatar da dakon mai, a sassan kasar.

Yanzu haka kungiyar ta IPMAN ta yi barazanar dakatar da sayar da man fetur, har sai gwamnati ta biya su basussukan da suke bin ta na dako akalla Naira biliyan 500.

Alhaji Bashir Ahmed DanMalam, shugaban IPMAN reshen Arewacin Nijeriya, a tattaunawarsa da manema labarai, ya ce, matsawar gwamnati ta gaza sauke nauyin da ke kanta, to kuwa za a shiga tsaka mai wuya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top