Samar da jirgin Rano Air, abin alfahari -Mamuda Zangon Kabo

RANO AIR

Tura wannan Sakon

Alhussain daga Kano

Abin alfahari da kuma farin ciki da samar da jirgin sama na Rano Air da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano ya samar da zai rinka zirga zirga a cikin kasar nan, wannan abin farin ciki ne matuka ga al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya.

Bayanin haka ya fito daga bakin wani mai taimakawa al’umma a jihar Kano sannan dan kasuwa da ke gudanar da harkokin kasuwanci a jihar, Alhaji Mamuda Liman Zangon Kabo, a lokacin da yake nuna farin cikinsa da wannan jirgi da AA Rano ya samar.

Alhaji Mumuda Liamn Zangon Kabo, ya kara da cewa, kamfanin na Rano Air, zai bunkasa tattalin arzikin jihar tare da samar da aikin yi ga al’ummar jihar musamman ga wadanda suka kammala karatunsu, baya ga samar da kudin shiga ga gwamnatin jiha da ta tarayya.

AA Rano ya zama zakaran gwajin dafi a harkar sufurin jirgin sama, kananan ‘yan kasuwa za su yi alfahari da samar da kamfani domin za su samu saukin zirga-zirgar kasuwanci a yankunan kasar nan. Zangon Kabo, ya yi kira ga masu manyan ‘yan-kasuwa musamman na jihar Kano cewa, ya zama wajibi su yi koyi da Alhaji Auwalu Abdullahi Rano, wajen tallafa wa harkokin kasuwanci da kuma al’umma musamman marasa karfi.

Daga karshe, matashin dan kasuwar ya yi addu’ar Allah ya bai wa sababbin shugabannin da aka zaba tausayi da rikon amana tare da kwatanta gaskiya wajen tafiyar da shugabanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *