Samun Mustapha Sule Lamido, alheri -In ji Indallah

Mustapha Sule Lamido

Mustapha Sule Lamido

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

An bayyana takarar neman gwamnan jihar Jigawa da Mustapha Sule Lamido San turakin Dutse a matsayin alheri ga al’ummar jihar I nji Indallah.

Jawabi ya fito ne daga bakin shugaban Gobe Ta Allah ce na jihar Jigawa, Alhaji Adamu Indallahi a lokacin da yake ganawa da manema labarai ciki har da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano a makon da ya gabata.

Tabbas samun matashi kamar irin San Turakin Dutse a matsayin gwamna a jihar Jigawa ci gaba ne, domin kyan da ya gaji ubansa sanin kowa ne cewa, Mustapha Sule Lamido jajirtacce ne, mai hangen nesa ne, mai karamci ne da kuma tunani.

Indallahi ya bayyana tafiyar San Turaki a matsayin hawan jirgin Annabi Nuhu duk wanda ya hau ya tsira kuma ya yi kira ga ‘yan jam’iyar PDP da ke jihar Jigawa da su hada kansu domin samun nasarar zabe 2023 ga jam’iyar PDP.

Indallahi ya bayyana gwamna Badaru Abubakar a matsayin wanda baya cika alkawari domin duk alkawarin da ya yi wa al’ummar jihar Jigawa ya saba, domin a yanzu haka Jigawa ita ce koma baya wajen harkar ilimi da rashin kamfanoni da asibiti da hanya da kuma makamantansu, domin haka ya yi kira al’ummar jihar da su zabi jam’iyar PDP a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *