Samun shugaba tamkar Buhari, alheri -Umaru Hussaini Gabari

Shugaban Kasa Buhari
Daga Musa Diso
Shugaban kungiyar kula da da jin dadin ‘yan-kasuwa ta kasa, Alhaji Umaru Hussaini Gabari Kiru ya ce, samun shugaba irin Muhammad Buhari a Nijeriya alheri ne da kuma ci gaban al’umma.
Ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilin jaridar Albishir a babban birnin Kano satin da ya gabata.
Ya ce, cikin shekara 8 da shugaba Buhari ya yi an samu nasarori da ci gaba musamman a Arewa domin a lokacinsa ne akai titin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna daga Kaduna zuwa Kano da kuma uwa uba titi wanda ya dauka daga Kano zuwa Abuja ba shakka wannan babbar nasara ce, da kuma kalubale ga sauran shugabanni da suka gabata ya kuma kara da cewa, a zamanin Buhari ne ake tozarta duk wanda yaci hanci da rashawa kuma ya saci kudin gwamnati savanin da don haka ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su ci gaba da addu’a da kuma fatan samun shugaba irin Buhari a kasar nan.
Alhaji Umaru ya nuna goyon bayan sa ga irin matakin da gwamnati jihar Zamfara ta dauka cewa, kowa ya kare kansa kuma ya mallaki binduga ba shakka wannan abu ya dace domin ta haka ne kawai za’a kawo karshen al’amari.
Ya ce, wannan annoba ba wai kawai a Nijeriya ba ne duk duniya domin haka ya yi kira ga al’umma da su ci gaba da addu’a ta samun sauki domin kawo karshen al’amari. Shugaban ya ce, halin da ake ciki a Nijeriya na tsadar kaya da kuma tashin abu ne wanda ya shafi duniya ba Nijeriya ba kawai, Saboda haka ya yi fatan Allah ya sa Nijeriya ta samu shugaba irin Buhari nan gaba domin gina kasa da ci gaban al’umma.