Sanata Lawan ya taya Buhari murnar cika Shekaru 78

Sanata Lawan ya taya Buhari murnar cika Shekaru 78
Tura wannan Sakon

Sani Gazas Chinade Daga Damaturu

Shugaban majalisar Dattijan Ni­jeriya, Sanata Ahmad Ibrahim Lawan mai wakiltar Arewacin Yobe, ya taya shugaban kasa, Mu­hammadu Buhari murnar cika shekaru 78 da haihuwa, wanda ya yi daidai da ranar Alhamis da ta wuce.

Shugaban majalisar dattawan, ya bayyana hakan ne cikin wata takardar sanarwa ga manema labarai wadda ofishin sa ta fitar kana kuma wadda ya rattaba wa hannu, inda ya bayyana ranar a matsayin mai muhimmanci ga dukkan ‘yan Nijeriya.

A cewarsa yana mai nuna farin cikin haduwa da ‘yan uwa da iya­lai, abokai, da jami’an gwamnati, na huldar yau da kullum da shugaban kasa wajen taya shi murnar wannan muhimiyyar rana wadda yake bikin tunawa da cikar sa a wannan matsayi na shekaru 78 a cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.

Ya jaddada cewa, duk shekarun da shugaba Buhari ya yi, bai gushe ba yana gudanar da shugabancin kasar nan cike da nuna cikakkiyar jajirce­war sa wajen ganin ya samar da hadin kai, zaman lafiya da ci gaban Nijeriya tare da samarwa ‘yan kasa walwala.

Shugaban majalisar ta dattawa ya kara da cewa, wannan ya kunshi sa­mar wa ‘yan kasa abubuwan more ra­yuwa, tsare-tsare na musamman wad­anda za su taimaki masu karamin karfi da bunkasar tattalin arziki da walwa­lar ‘yan Nijeriya, wanda shugaba Bu­hari ke kokarin kwatanta gaskiya da kimarsa a idon talaka tare da dora lamurran su sau da kafa wajen ganin ya kai kasar nan bisa tudun tsira.

Don haka ya yi kira ga dukkan ‘yan kasa su fadada tunanin su da hangen nesa, kana su ci gaba da tsay­awa kafada da kafada tare da bayar da cikakken goyon baya ga manufofin gwamnatin shugaban kasa a wannan aiki da yake yi wajen sanya matukar kishin kasa a zukatansu.

A cewarsa a matsayi na na dan jama’iyyar APC, ya zama wajibi ya nuna farin ciki da yadda shugaba Buhari ya yi damara wajen aiwatar da gyare-gyare da sake gina wannan kasaitacciyar jama’iyyar APC domin ganin ta cim ma burinta na shugaban­tar Nijeriya a cikin kyakkywan yanayi tare da ci gaban mulkin dimukradiyya da tattalin arziki na tsawon lokaci.

A bangaren ‘yan majalisar dokoki na Tarayya, Jam’iyyarsu ta APC za mu ci gaba da aiki cikin tsanaki da kwan­ciyar hankali tsakanin mu da bangaren zartarwa domin samun dauwamam­men zaman lafiya da ci gaban Nijeriya da al’ummarta baki daya kamar yadda hakkin hakan ke wuyansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *