Sarkin Fika ya ziyarci sarkin Kaltungo -Da zummar zumunci

Sarkin Fika ya ziyarci sarkin Kaltungo
Yusuf Tata Daga Damaturu
A makon da ya gabata sarkin Fika, kuma shugaban majalisar sarakunan jihar Yobe, Alhji Mohammad Abali Ibn Mohammad Idrissa ya kai ziyarar karfafa dankon zumunchi tsakanin masarautun Fika da masarautar Kaltungo ta sarki.
Injiniya Saleh Mohammad Umar, wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar sarakunan jihar Gombe, sarkin Fika ganin yadda dubban jama’ar masarautar Kaltungo suka yi dafifi maza da mata, manya da kanana, ma’aikata da ‘yan-kasuwa dama wadanda suka zo daga gurare daban-daban, musamman domin yi masa marhabun da isowa ya ce, yana cike da farin cikin da ba zai misaltuba.
Sarkin Fika ya ce, wannan wata rana ce da ba zai taba mantawada itaba a rayuwarsa kuma itace ranarda zumunchi tsakanin masarautun biyu ya tabbata, Sarkin na Fika yayi addu,ar dorewar wannan zumunchi da suka kulla a tsakanin masarautunsu da fatan Al,ummarsu suyi koyi dasu ta hanyoyi daban daban, masarautar Fika a cewar sarkin masarauta ce mai rungumar kowane mutum da karramashi tamkar danta, bama kyamar baki kofofinmu suke kowane lokaci,a wannan daren sarkin Kaltungo Injiniya Saleh Mohammad Umar ya shirya wasannin gargajiya, domin nuna farin cikinsa dana al’ummarsa ga babban bakonsa inda aka yi kade-kade da bushe-bushe na al’adun masarautarsa.