Sarkin Kano Ya Gamsu Da Asibitin Labanawa Mazauna Kano

Tura wannan Sakon

Daga Hassan Muhammad

Maimartaba sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayyana gamsuwarsa da asibitin Nijeriyan Labanis Hospital da cewa, ya dace da kudurin gwamnati wajen kula wa marasa lafiya da sauwake masu fita waje domin neman lafiya.

Sarkin ya yi furucin a lokacin da ya kai ziyara asibitin, ya bayyana gamsuwarsa da irin na’urorin zamanin da aka zuba a asibitin. Ya ce, haka zai kawo sauki da ci gaba a harkokin lafiya.

A nasa jawabin shugaban asibitin, Abbas Hajjaj ya ce, asibitin an samar da shi ga marasa lafiya na jihar Kano da ma wajenta domin saukaka masu da kuma samun saukin kudin jirgi zuwa neman magani kasashen waje.

 Ya kuma gode wa Maimartaba sarki bisa kulawarsa ga harkokin lafiya. A wani ci gaban kuma, kungiyar masu maganin gargajiya mai shimfida bisa jagorancin Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babba sun mika ta’aziyyarsu ga tsohon gwamnan Kano, Sanata Kabiru Ibrahim Gaya bisa rasuwar dansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *