Sarkin Kano ya sami lamba mafi daukaka a Senegal

Sarkin Kano ya sami lamba mafi daukaka a Senegal

Sarkin Kano Aminu Ado Bayero

Tura wannan Sakon

Daga Mahmud Gambo Sani

A ranar Litinin da ta gabata, shugaban kasar Senegal, Mista Macky Sall ya karrama Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da lambar girma mafi daukaka a kasar Bikin wanda aka gudana a fadar gwamnatin kasar, ya sami halartar mukarraban gwamnati da ‘yan tawagar sarki.

A jawabinsa na karbar lambar girmamawar, Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero, ya ce, lambar girmamawar da kasar Senegal ta ba shi, girmamawa ce ga masarautar Kano da al’ummar jihar Kano da kuma Nijeriya baki daya. Kasar Senegal na da lambobin girmamawa guda biyu.

Ta farko ita ce wadda ake kira a turance da National Orders of the Lion, wadda akan bai wa wadanda suka bayar da gudummawa ta musamman, sai kuma lambar girmamawa ta biyu wadda ake kira da Order of Merit, wadda akan bai wa mutanen da suka bayar da wata gagarumar gudummawa.

A nan mu ma rukunin jaridun Triumph muna taya Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero, murnar samun wannan babar lambar girmamawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *