Sarkin Musulmi ya yi wa ‘yan siyasa nasiha ta uba -A kan yakin neman zabe

, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III

Tura wannan Sakon

Musa Lemu Daga Sakkwato

Mai alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar na III ya ja kunnuwan ‘yan takara na jam’iyyu daban-daban da su kasance sun samar da zaman lafiya a yayin da suke ci gaba da yakin neman zabe.

Mai alfarman ya bayyana haka ne a lokacin da yake maraba lale da dan takarar gwamnan jihar Sakkwato a karkashin jam’iyyar APC, Alhaji Ahmad Aliyu a lokacin da ya kai masa ziyarar ban girma a fadarsa da ke Sakkwato jim kadan kafin fara yakin neman zabe a jihar..

Sarkin Musulmi ya kuma gargade su da su kasance mutane nagari wadanda ke bin doka da oda a lokacin da suke ci gaba da neman goyan bayan jama’a tare da yin kira da magoya bayansu da su bi tafarkin neman zaman lafiya domin ci gaban jihar. Mai alfarman ya kuma jinjina wa APC ganin yadda ta zabo dan takarar da ya dace ga al’ummar Sakkwato a inda ya yi addu’a domin a gudanar da yakin neman zabe lafiya har a kai ga nasara.

A lokacin da yake jawabi a wajen taron neman zaben dan takarar gwamnan na APC a shekarar 2023 a garin Gwadabawa a ranar Litinin da ta gabata babban daraktan neman zaben na jam’iyyar, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi ya ce, kafin fara yekuwar neman zaben na su sai da suka kai gaisuwar ban girma ga mai alfarma Sarkin Musulmi domin neman albarka da tabarraki.

Maigari Dingyadi wanda har wa yau shi ne ministan harkokin ‘yan-sanda na kasa ya ce, sun je fadar mai alfarma domin neman tabarraki a inda ya ja kunnen su tare da yin fatan alheri da kuma jinjina da shawara na a guji yin batanci ko zage zage.

Babban daraktan ya bayyana cewa, jam’iyyar su ta APC jam’iyya ce da take kamanta adalci da gaskiya a tsakanin al’umma a inda a dalilin hakan ya sanya jama’a suke ci gaba da tururuwa suna caja sheka zuwa jam’iyyar APC A nasa jawabi shugaban APC na jihar, Alhaji Isa Sadik Achida ya yi bayanin ireiren manyan ayyukan da tsohon gwamnan jihar, Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko ya gudanar wanda har wa yau shi ne uban jam’iyyar APC.

Achida ya ce, ayyukan alherin da tsohon gwamnan ya gudanar ga al’ummar Sakkwato Lungu da sako sai dai jinjina a sabo da haka yabon gwani ya zama dole. Shi kuwa a nasa jawabi dan takaran gwamnan, Alhaji Ahmad Aliyu ya jera alkawari 8 na ayyukan da zai gudanar ga al’ummar jihar da zarar an zabe shi ya zama gwamnan jihar Sakkwato da yardar Allah.

Ya ce, wadannan ayyuka za a bisu daya bayan daya domin tabbatar cewa, an gudanar das u babu jibge ayyukan da suka hada da fannin lafiya da ilimi da samar da wadataccen ruwan sha da fannin gona kazalika da bayar da hakkin shugabanin kananan hukumomi.

Dan takarar ya ce, da zarar an zabe shi zai tabbatar cewa, ya samar da ayyuka ga matasa, kazalika da kyautata jindadin rayuwar malamai da masu lalura na musamman inganta rayuwar ma’aikata da kyautata rayuwar malaman addini na jihar. Ahmad Aliyu ya yi kuma kira ga jam’a da su tabbatar sun inganta katin zaben su tare da adana su su kuma sun tabbatar cewa, sun jefa kuri’ar su ga jam’iyyar APC.

Daga karshe, jam iyyar ta kaddamar da yekuwar yakin neman zaben ta a kananan hukumomin Bodinga da Gwadabawa da Tangaza da kuma karamar hukumar Gudu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *