Sarkin Rano ya jinjina wa gwamantin Kano -Saboda ayyukan raya kasa

Alhaji Muhammad Kabiru Inuwa (Autan Bawo) sarkin Rano
Tura wannan Sakon

Abubakar Garba Isa Daga Rano

Maimartaba sarkin Rano, Dokta Kabir Muhammad Inuwa ya bayyana godiyarsa ga Allah da kammala azumin Ramadan na bana a jawabinsa ga dubban al’ummar Musulmi a fadarsa bayan kammala sallar karamar idin bana wanda babban limamin masallacin karamar hukumar Rano, Imam Kabir Muhammad ya agoranta a babban masallacin idin garin Rano.

Maimartaba sarkin ya kuma bayyana godiyarsa ga gwamnatin jihar Kano da take bai wa masarautar kulawa ta fuskar samar mata da managartan ayyuka sababbin tituna a cikin sabon garin Rano da kulawa da masarautare da babban asibitin Rano.

Maimartaba sarkin Rano ya kuma yi kira ga al’ummar masarautar Rano da su ci gaba da bayar wa gwamnati goyon baya da yadda take bayar wa harkokin ilimi lafiya da tsaro kulawa da ci gaban al’umma tare da kai rahoto ga duk bakuwar fuskar da ba su amince da ita ba ga hukuma mafi kusa.

 Ya kara da cewa, ya bukaci al’ummar musulmi da su kasance masu ci gaba da yin addu’o’i da Istigifari da yawan amfani da darussan da suka koya a watan Ramadan, tare da kira ga al’umma wajan gyaran magudanan ruwa da tsabtar mahalli duba da ga batowar damina.

Shi ma babban limamin masarautar Rano, Imam Kabir Muhammad ya jagoranci Sallar Idin karamar a cikin hudubarsa ya bayyana muhimmancin Zakkar fiddakai da falalarta ga al’ummar Musulmi. Babban limamin ya kuma bayyana falalar ranar karamar sallar idi ga dukkan al’ummar Musulmi inda ya ja hankali ga al’ummar Musulmi ga irin farin cikin da ni’imar da ke tattare ga al’ummar Musulmi a ranar.

 Tunda farko a nasa jawabin, bayan kammala sallar idin, Alhaji Usman Alhaji wanda shi ya wakilci gwamnan jihar Kano ya bayyana sakon gwamnan jihar Kano na taya murna ga masarautar Rano na kammala azumin Ramadam cikin nasara .

Ya kuma bukaci al’ummar Musulmi da su taimaka wajen ci gaba da addu’o’i domin samun zaman lafiya tare da gudanar da ayyuka daban-daban da gwamnati ta yi ta wajen inganta rayuwar al’umma.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back To Top