Saudi Arabia ta yi wa Benzema tayin miliyan 400

Tura wannan Sakon

Wadansu majiyoyi na nuna yiwuwar dan wasan gaba na Real Madrid Karim Benzema na shirin komawa Saudi Arabia da taka leda bayan karewar kwantiraginsa da kugiyar.

Sashen labaran wasanni na ESPN ya bayyana cewa Saudi Arabia ta yi wa Benzema tayin kwantiragin shekaru 2 kan farashin yuro miliyan 400 don komawa lig din kasar da taka leda a watan Janairu, wanda zai bashi damar hadewa da Cristiano Ronaldo na Portugal da ya koma Al Nassr da taka leda bayan raba gari da Manchester United a karshen waccan kakar.

Benzema dan Faransa mai shekaru 35 da ya lashe kyautar Ballon d’Or a shekarar 2022 wasu bayanai sun nuna cewa dan wasan ya cimma yarjejeniya da Madrid don tsawaita kwantiraginsa zuwa karin shekara guda a nan gaba.

Madrid dai ta gamu da mummunar kaka a wannan karon bayan rasa kofunan La Liga da zakarun Turai sakamakon mummunan san kaye hannun Manchester City a wasan gab da na karshe ko da ya ke ta yi nasarar lashe kofin Copa Del Rey.

Baya ga Benzema Saudiya na kuma harin manyan ‘yan wasan da suka kunshi Lionel Messi da Sergio Buskuets da Jordi Alba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *