Sauya sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya, dagajin siyasa -Sanata Bukar Abba

Sanata Bukar Abba

Sanata Bukar Abba

Tura wannan Sakon

Sani Saleh Chinade Daga Damaturu

Tsohon gwamnan jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim ya kalubalanci ‘yan siyasar da ke barin jam’iyyun su na asali ke canza sheka ya zuwa wadansu jam’iyyun domin biyan bukatar kan su da cewa, su masu irin dabi’ar tamfar ‘yan dagajin siyasa ne da suka shiga siyasa domin biyan bukatar kansu ba don talakawa ba.

Sanata Bukar Abba ya bayyana hakan ne a tattaunawarsa da manema labarai a garin Abuja a sakamakon yadda wadansu ‘yan majalisun suke canza sheka ya zuwa wata jam’iyyar da ba ita ta kai su kan matsayin da su ke kai ba, domin tsananin nuna zarmiya da rashin sanin ya kamata.

Tsohon gwamnan Bukar Abba Ibrahim wanda shi ne a baya ya wakilci gabashin jihar Yobe a majalisar dattawa ta kasa, ya yi tir ne bisa ga irin yadda wadansu takwarorinsa suke kokarin yi na barin jam’iyyar da suka biyo ta kanta domin zama matsayin da suke ya zuwa wata jam’iyyar da suke hange tafi ta su.

Saboda haka tsohon Sanatan ya nemi da hukumomi da jam’iyyu da su samar da wata kwakkwarar doka da za ta Sauya sheka daga jam’iyya zuwa jam’iyya, dagajin siyasa -Sanata Bukar Abba haramta irin lamarin na rashin akida ganin cewa, hakan kan haifar da samun rudani ga harkokin siyasa, kuma muddin an samo bakin zaren magance tsallake-tsallake da ‘yan siyasa musamman masu rike da madafun iko ke yi to lalle harkokin dimukuradiyya za su karfafa.

“Ya kara da cewa, ‘yan siyasar da duk ka ga suna yawo tsakanin jam’iyyu to kuwa labudda za ka tarar da cewa, aksarin su ‘yan dagajin siyasa ne marasa alkibla ta kwarai wadanda suna siyasa ne kawai domin biyan bukatar kansu da kansu ba don al’ummarsu ba, kamar yadda na fada a baya.”

“Domin haka ne tsohon gwamnan ya jaddada cewa, matukar ba a samo bakin zaren dakatar da yawaitar canza sheka da ‘yan uwanmu ‘yan siyasa ke yi ba daga wata jam’iyya zuwa wata ba, ba kuma tare da wadansu kwararan dalilai ba to akwai matsala babba.” Ya ci gaba da cewa, “Ba wai na tabbatar da cewa, irin halayya na yawaitar canza sheka ana yi ne ba tare da dalilai ba, to amma a ganina hakan ba zai zama alheri ga kasa ba.”

“Kuma alal hakika a matsayin ‘yan’adam dole ne lokaci zuwa lokaci a rinka samun rashin fahimtar juna a tsakankanin al’umma, to amma duk da haka ban ga abin har ya kai ga canza sheka ba maimakon a tsaya a sasanta tare da cire son zuciya.”

Da manema labarai ke tambayar sa kan ko akwai yiwuwar wata rana ya canza sheka ya zuwa wata jam’iyyar da ba APC ba? A nan sai jagoran na APC ya amsa da cewa, “Ai ni mai akida ne da ra’ayi daya, domin haka fau-fau ba zan taba barin akidar ta ba ta kaifi daya da na ke ba a tsawon rayuwa ta.

” Tsohon gwamnan kuma tsohon dan majalisar dattawan ya kuma yaba wa majalisar kasa bisa ayyukansu, kana ya kuma kalubalanci mutanen da ke zargin ‘yan majalisar a matsayin ‘yan amshin shata domin kawai yin watsi da bukatunsu da cewa, suna bin bangaren gwamnati sau da kafa maimakon turjiya da cewa, aikin kawai ne.” In ji Bukar Abba.

“Ya kara da cewa, majalisun kasa na yanzu na taka muhimmiyar rawa wajen samar da dokokin da al’ummar kasa za su amfana, kuma babu wata kasa a duniya da za ta wanzu ba tare da dokoki ba. Saboda haka ban amince da cewa, ai majalisar kasa ‘yar amshin shata ne ga bangaren zartaswa ba.”

Tsohon sanatan ya kuma bayyanawa al’umma kudirin sa na sake tsayawa takarar kujerar majalisar dattawa a zaben da ke tafe a shekarar badi ta 2023 don dawowa majalisar da nufin ci gaba da bada gudummawar sa ga yankin sa, Jihar sa da kuma kasa baki daya na shekaru 4 kacal kafin ya yi murabus. Ya kara da cewa, “Na shafe kusan shekaru 12 a majalisar dattawa ta kasa, kana na kuma bar zauren majalisar kusan shekaru 3 na ga abubuwa masu yawa musamman kan abin da ya shafi harkokin tabarbarewar tsaro wadda ke da bukatar a yi gyare-gyare akai a kasa baki daya duk da cewa, sanin kowa ne majalisar dattawa ba ta da ikon gudanar komai dole sai da hadin bakin majalisar wakilai da kuma majalisar zartaswa a gefe guda.”

“Na kasance bana komai a tsawon shekarun nan uku duk da cewa, ina da dimbin gudummawar da zan iya bayarwa sakamakon dimbin sanin da na ke da shi kan harkokin tafiyar da lamuran al’umma. Hakan ne ya sa naga ya dace da in sake dawowa majalisar da yardar Allah domin ci gaba da bayar da gudummawata a 2023 wadda bayan shekaru 4 kuma na yi murabus a kashin kai na.”

Kan abin da ya shafi harkokin tsaron kasa kuwa, Sanata Bukar Abba ya ce, lalle akwai bukatar da shugaban ya rubanya irin kokarin da ya ke yi wajen ganin harkokin zaman lafiya ya inganta a kasar nan kafin cikar wa’adinsa.

Ya kuma kirayi ‘yan uwansa ‘yan siyasa da su zama masu hakuri tare da tausan zukatan mabiyan su, domin ganin an kaucewa fadawa cikin yanayin da ya yi hannin riga dangane da bukatun kasa cewa, kasa a halin da ake ciki na bukatar zaman lafiya kasacewa hatta harkokin na siyasa ma sai da zaman lafiya za a samu biyan bukatar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *