Sevilla na kokarin sayen Umar Sadik daga Almeria

Sevilla na kokarin sayen Umar Sadik daga Almeria

Umar Sadik

Tura wannan Sakon

Kungiyar Sevilla ta kasar Sipaniya tana tunanin daukar dan wasan gaban Almeria Umar Sadik, dan asalin Najeriya da ake ganin darajarsa ta kai Euro miliyan 25.

Yanzu haka Sadik na cikin ‘yan wasa da kungiyoyi irinsu Benfica, Ajad Amsterdam, da kungiyoyin Spain Vilarreal da Valencia ke zawarci.

A cewar wani rahoto da Marca ta fitar, Sevilla ta dade tana zawarcin dan wasan na Najeriya kuma duk da sun fahimci cewa darajarsa za ta karu a yanzu, ganin yadda kungiyar ta Andalus ta samu zuwa gasar La Liga, har yanzu suna sha’awarsa.

Dan wasan wanda haifaffen Kaduna ne a Najeriya ya buga wasanni bakwai a kungiyar da ya fara taka leda a Spezia kafin ya koma Roma a shekarar 2015 a matsayin aro na shekara daya, tare da abokin taka ledar sa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *