Sha’aban Sharada ya koma ADP

Tura wannan Sakon

Daga Rabiu Sanusi Kano

Dan majalisar wakilai mai wakiltar a hukumar birni da kewaye a jihar Kano, Alhaji Sha’aban Ibrahim Sharada, ya sauya sheka daga APC zuwa ADP domin samun damar tsayawa takarar gwamnan jihar Kano kamar yadda ya kudurta.

Batun hakan na zuwa ne lokacin da hukumar zabe mai zaman kanta ta mika masa takardar shedar takararsa a jam’iyyar ADP cewa, dan majalisar ya koma jam’iyyar ADP kuma ya karbi tikitin takarar gwamna na jam’iyyar da ya koma a halin yanzu domin cim ma muradinsa.

Majiya mai tushe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa watau INEC da ke jihar Kano ta ce, Sha’aban Sharada zai yi wa jam’iyyar ADP takara tare da abokin takararsa, Rabiu Bako wanda shi ma tsohon kwamishina ne a jihar.

Sha’aban Ibrahim Sharada wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar wakilai kan harkokin tsaro da leken asiri, ya yi takarar neman tikitin takarar gwamna a jam’iyyar APC amma mataimakin gwamnan jihar Nasiru Yusuf Gawuna ya samu nasarar lashe zabe a lokacin da aka gudanar da zaben fitar gwani.

A baya dan majalisar ya kasance cikin kungiyar G-7, a jam’iyyar APC karkashin jagorancin tsohon gwamna Ibrahim Shekarau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *