Shawo kan ‘yan-ta’adda, dawo da tsofaffin sojoji -Atiku

Shawo kan ‘yan-ta’adda, dawo da tsofaffin sojoji -Atiku

Shawo kan ‘yan-ta’adda, dawo da tsofaffin sojoji -Atiku

Tura wannan Sakon

Tsohon  Mataimakin Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dawo da tsofaffin sojoji a matsayin mafita ga kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta.

Atiku Abubakar, wanda shi ma tsohon dan takarar shugaban kasa ne, ya yi kiran ne a cikin wata sanarwar da ya fitar a kan tabarbarewar yanayin tsaro a ranar Talata da ta gabata.

Ya ce, yanayin tsaro a Nijeriya yana tabarbarewa cikin sauri kuma talakawan Nijeriya suna rayuwa cikin fargaba game da rayukansu da na‘ yan uwansu.

Babu wurin da ake da kwanciyar hankali, kama daga gonaki da kasuwanni da makarantu cikin gidaje da masallatai, majami’u, da kuma birane duk abin ya shafa, in ji shi.

Atiku Abukar ya kara da cewa, ‘yan ta’adda na ci gaba da fadada yankunansu a Arewa maso gabas, zuwa yankuna masu nisa har zuwa jihar Neja a Arewa ta tsakiya, mai nisan ‘yan tafiyar sa’o’i daga babban birnin tarayya Abuja.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce, yanzu lokaci ya yi da za a yanke hukunci game da shugabanci, inda ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi la’akari da tuna daukacin tsofaffin sojoji maza da mata, wadanda ke da niyyar komowa bakin aiki, domin taimaka wa dakarun da ke fafatawa da ayyukan tsageru ta kowace kusurwa, har sai sun samu nasara.

Ya ce, a matsayinsa na tsohon mataimakin shugaban kwamitin tsaro na kasa, yana sane da cewa, Nijeriya tana da dimbin gwarazan tsofaffin sojoji, wadanda suka samu horo a gida da waje kuma har yanzu suna nan da ransu”. Ya ce, babu wani amfani na barin damar ta sukurkuce, alhali kasa na cikin wani yanayi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *