Shekarau ya caccaki masu son dawo da siyasar dabbanci

Malam Ibrahim Shekarau
Tsohon gwamnan Kano, kuma Sanata mai wakiltar Kano Ta Tsakiya Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana damuwa a kan yadda wasu ‘yan siyasa a jihar ke kokarin farfado da siyasar daba da aka jima da kawar da ita.
Shekarau ya bayyana hakan ne yayin wata hira da Sashen Hausa na BBC, inda ya ce babbar illa ce a ci gaba da yin hamayyar siyasa a Kano kamar yadda ake ganin wasu na yi, ta hanyar daukar makamai suna far wa abokan hamayyarsu.
Yana magana ne kan batun fitar da wanda zai gaji gwamnan jihar mai ci Abdullahi Umar Ganduje a zaben 2023, inda ya ce akwai bukatar shugabannin jam’iyyar APC na jihar su yi wa kowa adalci, kada a hana duk mai sha’awa tsayawa takara. Ya ce “Babu laifi masu neman mukamai su fito, yau in masu neman gwamna sun kai mutum 100 karkashin jam’iyyar APC a Kano duk su fito, abun da kawai muke ganin zai zama illa shi ne ya zamana ana siyasar gaba, wannan kauyanci ne, shirme ne, kuma ya saba wa tarbiyyar addinin Musulunci ma”, in ji shi.