Shekaru 12 na wakilci: Muna kalubalantar Nasiru Ali Ahmad -Maryam Kamsaf

Nasiru Ali Ahmad da Maryam Kamsaf

Nasiru Ali Ahmad da Maryam Kamsaf

Tura wannan Sakon

Rabiu Sanusi Daga Kano

An bukaci danmajalisar karamar hukumar Nasarawa da ke jihar Kano da ya gabatar ma da al’ummar da yake wakilta ayyuka biyar da ya gabatar masu cikin shekaru 12 da ya kwashe yana wakilta a cikin yankinsa.

Bukatar haka ta fito daga bakin ‘yar takarar kujerar majalisar tarayyar karamar hukumar Nasarawa karkashin jam’iyyar ADC, Hajiya Maryam Muhammad Sani a wata zantawa da Albishir ranar juma’ar da ta gabata.

‘Yar takarar majalisar ta ce, tana bukatar dan majalisa mai ci a yanzu da ya zo ya nuna masu titi mai tsawon kilometer daya cikin shekarun daya shafe a matsayin wakilinsu, ko kuma wadansu ayyukan da zai bigi kirji ya ce, shi ya yi ba da aljihun gwamnati ba.

Haka zalika, Maryam ta kuma bayyana cewa yanayin yadda shugabanni suke mayar da mata saniyar ware babu wata kulawa ko ba su damar yin wani kokari ko yunkurin samar da ci gaba koda tsakanin matan ne amma karshe babu abin da matan ke karewa da shi daya wuce “Woman leader.”

“A yanzu haka idan da za a ilimantar da ‘ya’ya mata to lallai kamar ka ilimantar da sauran al’umma ne baki daya, sannan yanzu haka cikin karamar hukumar Nasarawa idan ka dauki hanyoyi watau tituna da sauran yadda ruwa ke ambaliya a cikin gidaje da unguwanni abi nda kowa ya san haka batun yake.”

Wajen batun lafiya kuwa ta ce, babu wani abin a zo a gani da ya yi a cikin asibitocin yankin na su, ya zuwa yanzu idan matsalolin rashin lafiya ya kama wata ko wani to lallai sai dai abin da hali ya yi domin babu kayan aiki ko wadansu magunguna a cikin kananun asibitoci nsu, balle uwa uba maganar haihuwa da kafin ma a isa asibitin ma saboda rashin kyawun hanyoyi a kan rasa rai.

Haka kuma sai batun taimakon mata da take ganin idan ta samu dama na lashe zaben kujera da mace da matan za su iya samu na gudunmuwar abubuwan alheri da yawancin masu mulki maza ba sa cika ba matan damar yi ba.

Kamsaf ta ce, lallai tun da siyasa ba ta haramta ga mata ba babu shakka za ta yi bakin kokarinta domin ganin ta lashe zaben kujerar majalisar tarayyar karamar hukumar Nasarawa da izinin Allah domin dora matasa kan turbar muntsira tare da ceto martabar karamar hukumar ta dama jihar Kano baki daya.

Daga karshe, ta bukaci mata kada su zama masu kasawa wajen neman damar da za’a dama da su kan tafiyar “YANCI” da zai taimaka wajen ceto al’umma daga halin da wadansu ‘yan siyasar ke jefa jama’a cikin halin “Kaka ni kayi”domi n azurta kansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *