Shekaru 23 da mulkin dimukuradiyya babu abin a-zo-a-gani -In ji Ashiru

Shekaru 23 da mulkin dimukuradiyya babu abin a-zo-a-gani

Tura wannan Sakon

Daga Musa Diso

Shugaban dattawan kungiyar masu motar kurkura na jihar Kano, watau (Mini Trucks Dribers Association) Alhaji Ashiru Abdullahi, ya bayyana rashin jin dadinsa dangane da yadda gwamnati, musamman gwamnatin jihar Kano ta yi watsi da ‘yan kungiyar wajen rashin tallafa musu.

Ya ce, cikin shekaru 23 da komawa mulkin dimokuradiyya a Nijeriya, babu wata gwamnati da ta taba zama da su kamar yadda ake yi a sauran makaftan jihar Kano.

Alhaji Ashiru Abdullahi, ya yi wannan bayanin ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ofishinsa dake kan titin IBB a birnin Kano, a makon da ya gabata.

Ya kara da cewa, daga lokacin da aka kafa kungiyar zuwa yanzu, ta sami nasarori daban-daban, musamman wajen samar da ayyukan-yi ga matasa domin dogaro da kai, inda ya ce, kungiyar ta tura matasa makarantu daban-daban domin karo karatu.

Ashiru ya bayyana dangantakar da ke tsakanin jami’an tsaro musamman ‘yan sanda a matsayin kyakkyawar dangantaka, inda ya yaba wa kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, bisa karrama kungiyar da ya yi wajen zaman lafiya da son ci gaban al’umma.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnatin jihar Kano ta tallafa musu kamar yadda sauran jihohi suke yi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *