Shin ka san ‘yan Taliban?

Yan talban

Tura wannan Sakon

Taliban ta mulki Afghanistan daga 1996 zuwa 2001 inda ta gudanar da mulkinta karkashin shari’ar Musulunci a kasar. Ga wasu daga cikin muhimman abubuwa da suka shafi akida da tarihin kungiyar.

Yadda Aka Kafa Kungiyar Taliban? Taliban, na daya daga cikin kungiyoyin da ke fada a yakin basarar da ya kaure a Afghanistan a shekarun 1990 bayan da Tarrayar Sobiet ta janye daga kasar. Kungiyar ta bayyana ne a shekarar 1994 a birnin Kandahar da ke kudancin Afghanistan.

Sunan shugaban da ya kafa ta Mullah Mohammad Omar, wani limami a birnin, wanda ya jagoranci mayakan kungiyar har iya karshen rayuwarsa a 2013. Mene Ne Alakarta Da Amurka? Kungiyar Taliban ta kafu ta hanyar daukan mayakan kungiyar Mujahedeen da suka yi fada da sojojin Sobiet.

A shekarun 1980 Amurka ta tallafawa kungiyar ta Muhajahedeen a fadan da take yi da sojojin tarayyar ta Sobiet. Ta Yaya Kungiyar Taliban Ta Kafa Gwamnati? Bayan da dakarun tarayyar Sobiet suka janye daga Afghanistan a shekarar 1989 da kuma rugujewar gwamnatin kasar, Afghanistan din ta fada cikin kangin yakin basasa.

Taliban ta yi ta neman goyon bayan ‘yan kasar tare da yin alkawarin za ta maido da doka da oda da tabbatar da adalci. A shekarar 1994, ta karbe ikon birnin Kandahar ba tare da wata kwakkwarar turjiya ba, sannan a 1996 mayakan kungiyar suka karbe ikon Kabul, babban birnin kasar.

Wacce Irin Akida Taliban Ta Runguma? Taliban na aiki ne da dokokin shari’ar Musulunci. Kashe mutane a baina jama’a da yin bulala ga masu aikata laifi ya kasance ruwan dare, sannan an haramtawa mata yin aiki da karatu baya ga tilasta masu da ake yi su saka burka idan suna cikin jama’a.

Kungiyar ta Taliban ta haramta amfani da litattafan kasashen yammacin duniya, sannan sun lalata duk wasu kayayyakin tarihin gargajiyar wasu al’umomi, ciki har da wani gunki mabiya addinin Buddha mai shekara 1,500 a yankin tsaunin Bamiyan. Mene Ne Alakarsu Da alKaida? Taliban ce ta ba shugaban kungiyar tsageru ta alKaeda, Osama bin Laden mafaka.

Al Kaeda ta kafa sansanonin horarwa a cikin kasar ta Afghanistan, inda take ba mayakanta masu kai hare-hare ta’addanci a sassan duniya horo, ciki har da harin 11 ga watan Satumba na shekarar 2001 da aka kai kan Amurka. Ya Aka Yi Mulki Ya Kubuce Mata? Kasa da wata daya bayan harin 11 ga watan Satumba, Amurka da kawayenta suka mamaye Afghanistan.

Izuwa farkon watan Disamba, an kawar da gwamnatin Taliban, inda Amurka ta hada kai da ‘yan kasar don kafa gwamnatin dimokradiyya. Me Ya Faru Bayan Haka? Bayan da aka kawar da su, shugabannin Taliban sun tsere zuwa inda suka fi wayo – kudanci da gabashin kasar ta Afghanistan wasu kuma suka fantsama zuwa cikin Pakistan.

Daga nan sai kungiyar ta fara kai hare-hare akan gwamnatin Afghanistan da Amurka ke goyon baya, inda ta kan yi amfani da bama-bamai hadin gida da kuma kai hare-haren kunar bakin wake.

A 2020, gwamnatin Amurka ta kulla yarjejeniya da Taliban bayan kwashe shekara 20 da mamaye Afghanistan. Matsayar da aka cimma, ta shata wani jadawali kan yadda Amurka za ta janye dakarunta daga kasar inda ita kuma Taliban ta yi alkawarin za ta daina kai hare-hare akan Amurka sannan za ta zauna a teburin sulhu da gwamnatin Afghanistan. Sai dai a cikin watanni da aka kwashe ana tattaunawa tsakanin Taliban da gwamnatin Afghanistan an gaza samun mafita kan yadda za a kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Wadanne Kasashe Ne Suka Aminta Da Taliban? Kasashe kalilan ne suka amince da gwamnatin Taliban a lokacin da take mulki a tsakanin 1996- 2001, wadanda suka hada da Pakistan, Hadaddiyar Daular Larabawa da Saudi Arabia.

Babu wani abu da ya nuna tabbacin cewa ko sauran kasashe da dama za su amince da sabuwar gwammatin Taliban, sai dai Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken ya fada a 2021 cewa, Afghanistan za ta zama kasa mai mulkin kama karya idan har Taliban ta karbi mulki da karfin tuwo da aikata ta’asa.

Yadda Taliban Ke Samun Kudade Bayan shekara 20 tana yakar sojojin Amurka da na kasashen hadin gwiwa, Taliban ta kwace iko a Afghanistan, kasar da aka hambarar da gwamnatin kungiyar a 2001.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *