Shirin maidakin gwamnan Kano kan lafiya, ya yi nasara – Bincike

Tura wannan Sakon

Daga Jabiru Hassan

Babu shakka, shirin kula da lafiyar mata da kananan yara na uwargidan gwamnan jihar Kano, watau “ Professor Haf­sat Abdullahi Umar Ganduje Women Health care delivery” yana cim ma gagarumar nasara, musamman yadda kwararrun likitoci suke za­gayawa mazabu da garuruwa suna duba mata da basu ma­gunguna kyauta domin talla­fawa harkar lafiyarsu.

Shirin yana kara bai wa mata masu juna biyu da kuma sauran masu dauke da larurori daban-daban damar bayyana abubuwan da ke damun su ga kwararrun likitocin da ke shiga sako-sako da kuma lun­guna, domin samar masu da magunguna ko kuma sahihan shawarwari na magance wad­annan cututtuka wanda hakan abin a yaba ne.

Wakilinmu wanda ya gu­danar da wani bincike dan­gane da yadda shirin kula da lafiyar matan ke tafiya, ya ru­waito cewa, tawagar kwarar­run likitocin sun sami nasarar ziyartar mazabu masu tarin yawa da ke yankin karamar hukumar Dawakin Tofa kuma tare da duba mata masu yawan gaske ba tare da wata matsala ba, wanda hakan ya nunar da cewa, shirin kula da mata na uwargidan gwamnan jihar Kano yana tafiya yadda ake bukata.

Albishir ta sami jin ra’ayoyin al’umma dangane da shirin na kula da lafiyar mata inda dukkanin wadanda suka zanta da wakilinmu sun nunar da cewa, wajibi ne a jinjinawa maidakin gwamna, Dokta Hafsat Abdullahi Umar Ganduje saboda wannan ko­kari nata na kyautata lafiyar mata da kananan yara a jihar Kano ba tare da nuna gajiya­wa ba.

Haka kuma mafi yawan matan da suka karbi magun­guna suka kuma yi amfani da shi sun bayyana cewa, sun sami waraka daga abubuwan da suke damun su musamman ganin cewa, kwararrun likitoci ne suka duba su tare da ba su magunguna ingantattu domin samun lafiya kan larurorin da ke damun su da iyalinsu.

A mazabar Gargari da ke karamar hukumar Dawa­kin Tofa, tawagar likitocin ta tsaya a garin Dungurawa kuma sun duba mata masu dimbin yawa tare da basu ma­gunguna bisa yanayin cututtu­kansu kuma cikin yanayi mai matukar gamsarwa duba da yadda aka yi aikin cikin sanin ya kamata, wannan mata sun fita sosai sun gana da wadan­nan likitoci ba tare da samun wani jinkiri ba.

Da yake tsokaci dangane da shirin na uwargidan gwam­nan, jagorar tawagar likito­cin Dokta Yusuf Sa’ad Hayin Hago ya ce, ko shakka babu suna samun nasarori wajen fitowar mata masu juna biyu da wadanda suke da wad­ansu larurori a tare da su bisa jagorancin mai bai wa gwam­nan kano shawara kan manu­fofin gwamnati da ci gaban al’umma, Alhaji Kabiru Inu­wa Hayin Hago.

Ya ce “ muna alfahari cewa, Kabir Hayin Hago yana kokarin tabbatar da nasarar wannan shiri mai muhim­manci wanda uwargidan gwamnan jihar Kano ta as­sasa domin kyautata lafiyar matan jihar Kano, sannan da yardar Ubangiji za mu yi aiki da amana domin ganin cewa, kwalliya tana biyan kudin sabulu a dukkanin mazabu 11 na fadin karamar hukumar Dawakin Tofa”. Inji shi.

Wadansu mata da suka sami ganin likitocin, Malama Rahimatu Aliyu da Fatima Umar sun godewa uwargidan gwamnan na kano saboda bi­jiro da wannan aiki da tayi wanda kuma ya zamo alheri ga mata masu ciki da kuma sauran mata da suka da wasu larurori a tare da su, sannan sun yi fatan alheri ga Alhaji Kabir Hayin Hago saboda bunkasa wannan shiri da yake yi ba tare da nuna kasala ba.

A nasa bangaren, mai bai wa gwamnan shawara kan manufofin gwamnati da ci gaban al’umma, Kabir Hayin Hago, ya ce “ wannan ko­kari na uwargidan gwamnan Kano, Farfesa Hafsat Abdul­lahi Umar Ganduje abin al­heri ne ga daukacin matan karamar hukumar Dawakin Tofa da jihar Kano baki daya, sannan ina sanar da cewa, za’a ci gaba da wannan aiki na kula da lafiyar mata tare da duba yiwuwar fadada shirin zuwa sauran yankunan kananan hu­kumomi domin bayar da tal­lafi kan kiwon lafiyar”. In ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *