Shugaba Buhari, damisar takarda -Sanata Rufa’i Hanga

shugaba buhari
Daga Musa Diso
An bayyana shugaban qasa Muhammadu Buhari a matsayin cewa ‘damisar takarda’ ce kawai, wanda babu ruwansa da halin da al’umma suke ciki sai kansa da iyalensa, a cewar tsohon sanata kuma xan takarar neman sanata a Kano ta tsakiya, a qarqashin ja m’iyar NNPP mai kayan marmari, Alhaji Rufa’i Sani Hanga.
Hanga ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai ciki har da wakilin Albishir, a gidansa da ke unguwar Bompai, a qaramar hukumar Nassarawa a birnin Kano, makon da ya gabata. Ya ce, tabbas Allah shi ne masani, domin rashin sani ne ya sa suka yi tallan Buhari a da, kuma yanzu ya bai wa ’yan Nijeriya mamaki, domin inda ake tunaninsa ba ta nan ya fito ba. Ya qara da cewa, ’yan Nijeriya da dama sun yi masa fatan alheri da ganin cewa varnar da PDP ta yi ta shekaru 16 zai kawo qarshenta, amma abun mamakin a nan, sai ga shi ya gaza, kuma cikin shekaru takwas da mulkinsa, babu wani abun a-zo-a- gani da ya yi wa ’yan Nijeriya na ci gaba, sai dai Allahwadarai.
Sanata Rufa’i Sani ya nemi afuwar ’yan Nijeriya a matsayinsa na tsohon shugaban jam’iyar CPC na qasa, wanda suka tallata Buhari lungu da sako na qasar nan, domin Shugaba Buhari, damisar takarda -Sanata Rufa’i Hanga ya zama shugaban qasa na rashin sani, ashe damisar takarda ce, ba Buhari ba ne na zamanin soja, domin a wannan lokacin su Tunde Idiyagbon ne suke mulki. Ya ce, tabbas Buhari ya bai wa xan takarar shugaban qasa qarqashin jam’iyar NNPP, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda qasa ce kawai a gabansu da kuma ci gaban al’umma, sannan za a sami makomar wannan qasa da hanyoyin da mai ci a yanzu, da su zo a yi fuska da fuska domin bayyana irin ayyukan da suka yi wa al’umma da kuma ci gaban da suka kawo a wannan mazava.
Sanatan ya ce, ya yi imanin cewa, babu wanda ya yi abubuwa na ci gaban al’umma kamar sa, domin ya yi aikin gwamnati wanda ya fara daga farko ya dangana har qarshe a aikin gwamnati, kuma ya yi riqon muqamai daban-daban na siyasa, wanda ya haxa da; shugabancin jam’iyyar CPC na qasa da makamantansu. Don haka, wannan ya ba shi damar sanin makamar aiki da kuma kwarewa da gogewa a harkar mulki da siyasa, inda ya ce, shi ba xan tagajan-tagajan ba ne a Nijeriya. Hanga ya ce, shi xan siyasa ne na kwarai, ba xan takara ba, domin akwai bambanci tsakani xan takara da xan siyasa. Xan siyasa shi ne wanda kullum yake tare da jama’a ba ya gajiyawa. Shi ko xan takara ba ka ganin sa sai bayan shekara hudu, sannan zai dawo neman takara na neman muqami. Sanatan ya qara da cewa, a cikin shekara 17 rabonsa da sanata, bai tava rabuwa da al’umma ba, kullum yana tare da su.
Daga qarshe ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zavi cancanta ba kuxi ba, domin Nijeriya a yanzu na buqatar mafita da kuma jagoranci nagari. ’yan Nijeriya kunya, kuma ya sa qasar nan cikin tsaka-mai-wuya wanda dole sai an sami jajirtacce kuma tsayayyen xan takara mai hangen nesa irin su Sanata kuma tsohon gwamnan jihar Kano, kuma za a bi wajen kawo qarshe wannan matsalar. Hanga ya ce, a matsayinsa na tsohon sanata na Kano ta tsakiya, ya qalubalanci duk tsofaffin sanatoci na Kano ta tsakiyar damai ci a yanzu, da su zo a yi fuska da fuska domin bayyana irin ayyukan da suka yi wa al’umma da kuma ci gaban da suka kawo a wannan mazava.
Sanatan ya ce, ya yi imanin cewa, babu wanda ya yi abubuwa na ci gaban al’umma kamar sa, domin ya yi aikin gwamnati wanda ya fara daga farko ya dangana har qarshe a aikin gwamnati, kuma ya yi riqon muqamai daban-daban na siyasa, wanda ya haxa da; shugabancin jam’iyyar CPC na qasa da makamantansu. Don haka, wannan ya ba shi damar sanin makamar aiki da kuma kwarewa da gogewa a harkar mulki da siyasa, inda ya ce, shi ba xan tagajan-tagajan ba ne a Nijeriya.
Hanga ya ce, shi xan siyasa ne na kwarai, ba xan takara ba, domin akwai bambanci tsakani xan takara da xan siyasa. Xan siyasa shi ne wanda kullum yake tare da jama’a ba ya gajiyawa. Shi ko xan takara ba ka ganin sa sai bayan shekara hudu, sannan zai dawo neman takara na neman muqami. Sanatan ya qara da cewa, a cikin shekara 17 rabonsa da sanata, bai tava rabuwa da al’umma ba, kullum yana tare da su. Daga qarshe ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su zavi cancanta ba kuxi ba, domin Nijeriya a yanzu na buqatar mafita da kuma jagoranci nagari.