Shugabancin Nijeriya: PDP ta yi wancakali da karba-karba

Tura wannan Sakon

Jam’iyyar PDP babbar mai adawa da gwamnati ta sanar da yin watsi da tsarinta na karba karba, inda ta bayyana cewa, daga yanzu kowanne dan Nijeriya na iya takarar shugaban kasa ba tare da la’akari da yankin da ya fito ba.

Bayan wani dogon zama da kwamitin da shugabannin jam’iyyar suka kafa domin nazari a kan bukatar soke karba-karba, kwamitin ya amince da yin watsi da tsarin daga zabe mai zuwa.

Kwamitin ya ce, ya dauki matakin ne bayan nazari a kan halin da ake ciki da kuma la’akari da cewa, jam’iyyar ta su a wannan lokaci tana adawa ne, yayin da take kokarin kwace iko daga jam’iyyar APC mai mulki.

Zuwa wannan lokaci, ‘yan takara 13 suka bayyana aniyarsu ta tsayawa takarar zaben shugaban kasa a karkashin jam’iyyar PDP.

Daga cikinsu akwai tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar da gwamnonin Sakkwato da Bauchi da Ribers da tsohon shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *