Shugabannin kananan hukumomi za su yi rantsuwar kama-aiki -A yau

A yau, gwamnan jihar Kano, Dokta Abdullahi Umar Ganduje yake jagorantar bikin rantsar da shugabannin kananan hukumomi 43 da aka zaba, a ranar 16 ga Janairu 2021.
Bisa ga dukkan alamu, shugabanni 43 za a rantsar, saboda rasuwar na Bebeji, Alhaji Ali Namadi Bebeji, wanda ya rasu bayan kammala zaben da ‘yan kwanaki.
Jihar Kano, kamar takwarorinta a tarayyar Nijeriya, tana da shiyyoyi uku na majalisar dattijai, Kano ta Arewa tana da yankunan kananan hukumomi 13, Kudanci na da guda 16, sai Kano ta tsakiya mai guda 15, bi da bi.
Idan aka juya kan sarautun gargajiya kuma, akwai masarautu biyar, wadanda suka hada da; Kano, da Bichi da Rano, da Gaya da kuma Karaye. Biyu daga cikinsu a iya cewa, farfado da su aka yi, watau Rano da Gaya, a yayin da biyu daga cikinsu kirkiro su aka yi, watau Bichi da Karaye.
Da yake musayar ra’ayi da editan Triumph, kwamishinan kananan hukumomin jihar, Alhaji Murtala Sule Garo, ya yi alkawarin cewa, ma’aikatarsa za ta bullo da dokar da za ta tilasta wa shugabannin kananan hukumomi, da mukarrabansu zama a yankunansu daban-daban, a maimakon yin wadari zuwa birnin Kano, babu gaira, babu dalili.