Sultan Abubakar ya yi wa Mukabalar Kano bara’a

Sultan Abubakar ya yi wa Mukabalar Kano bara'a
Tura wannan Sakon

Mai Alfarma Sarkin Musulmi,Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya yi watsi da amsa gayyatar da gwamnatin Kano ta yi masa kan ya halarci mukabalar da za a yi da Malam Abdul-Jabbar bisa dalilin cewa,yin haka tamkar kara masa yin suna ne kawai babu abin da ganawar za ta amfanar.

A wata takardar bayani da ke dauke da sanya hannun babban sakataren Jama’atu Nasril Islam,Dr. Khalid, Mai Alfarmar ya ce, gwamnatin Kano ba ta tuntubi wadanda suka dace ba, ai da ba ta shirya Mukabalar ba, musamman idan aka yi tsokaci da kalmomin da ke fitowa daga bakin Mal. Abdul-Jabbar na yi wa koyarwar Addini ta’annati da bakaken maganganu ga Annabi SAW da iyalansa da Sahabbansa Madaukaka.

A karshe,Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya shawarci gwamnatin Kano da rungumi tsarin hana ta’annatin aukuwa nan gaba, ganin cewa, rashin sanin ya-kamata da rashin hankali sun dabaibaye kalmomin da Abdul-Jabbar ke amfani da su cikin wa’azin da yake tara matasa yana yi masu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *