Super Cup: Madrid, Barcelona za su fafata ranar 12 ga Janairu

Super Cup: Madrid, Barcelona za su fafata ranar 12 ga Janairu

Super Cup

Tura wannan Sakon

Za a buga wasan daf da karshe a Spanish Super Cup tsakanin Real Madrid da Barcelona ranar 12 ga watan Janairun 2022.

 Daya karawar za a yi ne tsakanin Atletico Madrid da Athletic Bilbao ranar 23 ga watan Janairun 2022. Za a buga wasannin a filin wasa na King Fahd da ke Riyadh a Saudi Arabia.

Ana buga Spanish Super Cup ne tsakanin kungiyoyi hudun da suka yi fice a wasannin gasar Spaniya da ta gabata.

Atletico Madrid ce ta lashe kofin La Liga na bara, inda Real Madrid ta yi ta biyu a babbar gasar ta Sifaniya.

 Barcelona ce ta lashe Copa del Rey a kakar da ta gabata, sannan Athletic Bilbao ta yi ta biyu. Za a buga wasan karshe a Spanish Super Cup na bana ranar Lahadi 16 ga watan Janairu a dai filin na King Fahad da ke Saudi Arabia.

An fara Spanish Super Cup a 1982, kuma Real Sociedad ce ta lashe kofin, bayan da ta yi rashin nasara a wasan farko da ci 1-0 a hannun Real Madrid ranar 13 ga watan Oktoban 1982.

 A wasa na biyu ta doke Real Madrid da ci 4-0 ranar Talata 28 ga watan Disambar 1982. Jerin wadanda suka lashe Spanish Sup Cup: FC Barcelona 13 Real Madrid 11 Athletic de Bilbao3 Deportibo La Coruna 3 Atletico de Madrid 2 Sebilla FC1 Real Zaragoza1 Balencia C.F1 Real Mallorca1 Real Sociedad1

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *