Taɓarɓarewar tsaro: Nijeriya na bukatar addu’a -In ji IBB

Tsohon shugaban Nijeriya Ibrahim Badamasi Babagida

Tsohon shugaban Nijeriya Ibrahim Badamasi Babagida

Tura wannan Sakon

Tsohon shugaban Nijeriya Ibrahim Badamasi Babagida ya nuna matukar damuwa dangane da halin da kasar ta tsinci kanta na tavarvarewar tsaro.

A wata hira da ya yi da BBC, Ibrahim Babangida ya ce yanzu akwai bukatar ‘yan kasar su dage da addu’o’in samun sassauci daga kashekashen da suka yawaita a sassan kasar. Sannan ya jaddada bukatar bai wa jami’an tsaro hadin-kai don kakkave vatagari.

Tsohon shugaban kasar na mulkin soja, ya ce ya wajaba a janyo hankali a’lummar kasar da su nuna jajircewa da yin addu’oi da kyakkyawan fata ga Najeriya saboda ‘yan kasar ba su da wata kasa bayan ita.

“Tilas mu tabbabatar mun yi wa kasarmu addu’a domin neman hadin-kan kasa da al’umma baki daya,” in ji shi. IBB ya ce, ya yi wannan kiran ne saboda yadda ake samun karuwa da yawan tashetashen hankula a kasar.

Ya kara da cewa: “A duk lokacin da mutane suka kunna talabjin a Nijeriya labarin da ake ji shi ne kan tashin hankali.” Sai dai ya ce, duk da cewa, gwamnatin kasar da sauran mutane na kokari wajen shawo kan matsalar amma wani lokaci abin akwai ban tsoro. “Ya kamata mu koma ga Ubangiji mu roke shi ya yi mana afuwa ya kuma kawo mana karshen wadannan abubuwa,” a cewarsa.

Sai dai kuma tsohon shugaban kasar ya ce, akwai bukatar ganin gwamnatin ta dauki matakin gudanar da taron yin sulhu domin a ba wadanda suke ganin an yi masu laifi damar magana da kuma sasantawa.

Ya kara da cewa, matakin yana tasiri sosai wajan dawo da zaman lafiya a wadansu kasashen duniya IBB dai na ganin akwai bukatar a samu wani wuri da jama’a za su taru su kawo koke-kokensu kuma gwamnati ta dauki matakin da zai tabbatar da cewa hankalin mutane ya kwanta kuma za su yi hakuri don kasar ta ci gaba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *