Tabbas APC za ta lashe zaben 2023 –Tarda

Tinubu

Tinubu

Tura wannan Sakon

Labarai daga Musa Diso

Shugaban jam’iyar APC da ke mazabar Karo a karamar hukumar Ungogo a jihar Kano, Alhaji Garba Abdullahi Tarda yace ko shakka babu jam’iyar APC za ta lashe zaben 2023 a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce, tuni ‘yan Najeriya suka shirya tsaf domin ganin an sake zaben APC a shekara mai zuwa domin ci gaba da ayyukan alheri ga al’umma da kuma raya kasa.

Tarda ya yi furucin a lokacin da yake tattaunawa da wakilin jaridar Albishir a ofishinsa da ke Kasuwar Sabon gari satin dgogayya da jam’iyar APC a zaben 2023 domin cikin shekaru 8 gwamnatin APC karkashin shugabancin Muhammad Buhari ta taka rawar gani kwarai da gaske, musamman wajen sama wa matasa aikin da kuma dogaro da kai.

Ya kara da cewa, sanin kowa ne cewa, gwamnatin APC ta kawo tsare-tsare masu mahimmanci domin ci gaban al’umma da kuma kasa baki daya, musamman yaki da masu cin hanci da rashawa domin a zamanin Buhari duk wani bata gari ya shiga taitayin sa kuma.

Tarda ya ce, tafiyar Bola Ahmed Tinubu kamar hawan jirgin Annabi Nuhu duk wanda ya hau ya tsira kuma idan akaa ya gabata.

Ya ce, tabbas babu wata jam’iya a yanzu da za ta iya  antsar da Bola Ahmed Tinubu a shekara ta 2023 zai kawo abubuwan raya kasa da ci gaban al’umma masu mahimmanci domin haka ya yi kira ga ‘yan da su najeriya zabi jam’iyar APC a 2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *