Takarar 2023: Matashi ya amsa kiran al’ummarsa na fitowa

Daga Alhussain Kano
Wani matashin dan siyasa da ya fito daga jam’iyyar APC daga karamar hukumar Dala a jihar Kano, Mukhtar Nalele Kulo, ya amsa kiran al’ummar kan fitowa neman takarar dan majalisar jiha a zaven 2023 idan Allah ya kai mu.
Mukhtar Nalele, ya shaida wa jaridar Albishir cewa, matukar Allah ya sa ya samu nasara zai bayar da kulawa a kan ilimi da koyar da sana’oi ga matasan karamar hukumar Dala.
Kuma zai bakin kokarinsa wajen kawo karshen shaye-shaye da wadansu matasa ke yi da kuma kwacen wayar hannu da wadansu matasan ke yi rashin ilimi da sana’a ne suke haifar da wadannan abubuwa, domin matasa su ne kashin bayan ko wace al’umma.
Sannan kuma idan Allah ya so zai zama madubi daga cikin ‘yan siyasar jihar, babban abin da yake bukata daga al’ummarsa ita ce, addu’a da fatan alheri tare da goyon bayansu idan zave ya zo su kada masa kuri’ar su.
Kulo, ya yi amfani da wannan dama da jinjina wa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje a kan yadda yake bakin kokarin sa a kan ilimi lafiya da sauran muhimman aikace-aikace ga al’ummar jihar, duk wanda ya shigo jihar zai tabbatar da haka.
Daga karshe, ya yi kira da masoya da magoya bayansa da su tabbatar sun karvi katin zave domin da shi ne mutum yake zaven shugaban da ya ke bukata.